Connect with us

Uncategorized

Iyalin mutane shida 6 sun kone kurmus da wuta a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Abin takaici, wata gida a Jihar Kano ya kame da wuta har ya tafi da rayukan mutane shidda a cikin gidan.

A jiya Lahadi, 4 ga wata Maris, wata mumunar al’amari da auku a gida mai lamba 39, da ke hanyar Bawo ta shiyar Nasarawa Kwatas, a Jihar Kano. Inda wuta ta kame da wata gida har mutanen gidan sun kone kurmus da wuta duka.

A bayanin masu zama a unguwar; sun bayyana da cewa gidan ya kone ne kurmus da makwabcin su, Mista  Isaiah Jonathan da Matarsa, Yara ukku da ‘yar yarinyar da ke taimaka masu da aikin gida.

Sun kara bayyana da cewa, watakila wutar ya faro ne da falo kamin dada ya mamaye gidan a yayin da suke barci duka. “Muna jin kukar su a farko da neman taimako amma jim kadan sai muka ji shiru lokacin da wutar ya kame gidan duka”

“Mun yi kokarin balle kofar da tagar gidan amma bamu samu cin nasara da hakan ba” inji makwabtan Mista Jonathan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Kashe Kamun Wuta (Fire Service) ta Jihar Kano sun ribato ran wani daga konewar wuta

“A karshe Hukumar Kashe kamun wuta ta Jihar sun sami kashe wutar” inji Ofisan yada labarai ga jami’an ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, a bayanin sa da manema labarai.