Connect with us

Labaran Najeriya

Karanta Irin mutanen da shugaba Buhari yace zai nada a rukunin shugabancin sa ta biyu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da irin mutanen da zai sanya a shugabancin sa a wannan karo ta biyu.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

A wata zaman tattaunawa da liyafa da shugaban yayi da Mata da Matasa na Jam’iyyar APC a birnin Abuja, shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa wadanda ke da aminci da adalci ne kawai zai sanya a mulkin sa wannan karon.

“Masu adalci da aminci, da kuma masu sanya ci gaban kasa a zuciyarsu bisa son kai ne kawai zan sanya a shugabanci na a wannan karo ta biyu” inji Buhari.

Wannan itace bayanin shugaban a ranar Asabar da ta gabata a wajen zaman liyafar.

“Zan tabbatar da cewa ban kunyatar da ku ba a shugabanci na”

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa na shirye don samar da taki ga manoma a farashi mai kyan gaske don tallafa masu da aiwatar da hidimar aikin gonakin su da kuma don samu karuwa da bunkasa ga hatsi don rage yunwa a kasar.

Buhari ya kuma shawarci matasa da kafa kai ga aikin noma don rage yunwa da kuma bunkasa yawar hatsi a kasar Najeriya.

Karanta wannan kuma: Kalli Bidiyon Obasanjo yadda ya bar Najeriya a gurguje bayan nasarar Buhari