Labaran Najeriya
Yau mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kai shekara 62 ga haifuwa
A yau 8 ga watan Maris, 2019, Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaba Muhammadu Buhari ya kai ga tsawon shekaru 62 ga haifuwa.
Osinbajo mutum ne mai kwazo da fasaha da kuma halin mazantaka ga lamirin zuciya mai kyau. Kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a baya da a lokacin da Osinbajo yayi hadarin jirgin sama a Jihar Kogi.
“Na gode ga Allah irin mataimaki da ya bani. Mutumi mai hikima da kuzari” inji Shugaba Buhari.
Gwamnatin tarayya sun gabatar da gaisuwar su a shafin twitter ga Farfesa Osinbajo da taya shi murna da kai ga shekaru 62 ga haifuwa.
Happy 62nd Birthday, Vice President Yemi Osinbajo (SAN). @ProfOsinbajo
We celebrate you, Sir. 🎉🎉🎉🎉🎉🎉 pic.twitter.com/nObJcsRJFo
— Government of Nigeria (@AsoRock) March 8, 2019
Mun kuma gano wata bidiyo a Naija News Hausa a shafin twitter yadda Farfesa Osinbajo da matarsa ke wakar godiya ga Allah da kare iyalin, musanman shi Osinbajo da kai ga ranar yau a cikin tsawon shekaru.
Kalli bidiyon a kasa;
To the lover of my soul,
My Strong Tower,
My Jesus,
Thank you for 62 years! pic.twitter.com/qzayvw3Yfm— Prof Yemi Osinbajo (@ProfOsinbajo) March 8, 2019