Labaran Najeriya
Kalli bidiyon yadda Buhari ya sake leken kuri’ar matarsa Aisha a zaben Gwamnoni

Naija News Hausa ta gano da wat bidiyo inda shugaba Muhammadu Buhari a yau wajen zaben gwamnoni ya kara leken kuri’ar matarsa Aisha, kamar yadda ya yi wajen zaben shugaban kasa da aka yi a baya ranar 23 ga Watan Fabrairun, 2019.
Mun ruwaito ‘yan awowi a baya da cewa shugaban da matarsa sun halarci runfar zaben su a garin Daura missalin karfe 8:00 na safiya sun kuma jefa kuri’ar su ta zaben gwamnoni da gidan majalisar wakilan jiha.
A cikin bidiyon, an gano Buhari da leken matarsa kamar yadda yayi a baya
Kalli bidion;
President Muhammadu Buhari casting his ballot in the governorship and House of Assembly elections in Daura, Katsina state pic.twitter.com/IIXtDsghst
— APC Nigeria (@APCNigeria) March 9, 2019