Labaran Najeriya
Tun da Buhari ya ci zabe, Ba na tsoro ko da na fadi ga kujerar gwamna – inji El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a yau bayan da ya kada nasa kuri’ar ga zaben gwamnoni da ta gidan majalisar Jiha a runfar zabe ta lamba 024, da ke a Runka/Marnona, Angwan Sarki, Kaduna, ya ce “Ba na tsoron fadi ga lashe kujerar shugabancin jihar Kaduna ta karo biyu”.
Bayan da gwamnan da kuma dan takaran gwamnan Jihar Kaduna a karo ta biyu, Nasir El-Rufai ya jefa na sa kuri’ar, ya raba a shafin twitter da hotunan lokacin da yake kan layi don jefa kuri’ar sa.
Kalli hotunan;
I am delighted to join fellow citizens at my polling unit to cast my vote in the governorship and state House of Assembly elections pic.twitter.com/WbKZQeeAhV
— Nasir Ahmad El-Rufai (@elrufai) March 9, 2019
El-Rufai ya kara da cewa baya cikin tsananci ko damuwa. ko da ace ya fadi ga tseren takaran kujerar gwamna tun da Buhari ya riga ya lashe kujerar shugaban kasa.
“Ko da na fadi ga nawa takaran, na riga na samu aiki” inji shi da murmushi kamar da wasa yake.
Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Nasir El-Rufai ya fada da cewa ko da ya sanya Paparoma a matsayin abokin takaran sa ne, Kiristocin Jihar Kaduna ba zasu so shi da mulki ba.