Connect with us

Uncategorized

An kashe mutane 16 a Jihar Kaduna a wata sabuwar hari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna a ranar Litini da ta gabata sun gabatar da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun kashe mutane goma sha shidda (16) a kauyan Barde da ke yankin Maro, karamar hukumar Kajuru. Wannan lamarin ya faru ne washe garin ranar Lahadi bayan da aka kamala zaben Gwamnoni da Gidan Majalisar Wakilai a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa   da cewa Jam’iyyar PDP sun isar da gaisuwar ta’aziyya ga iyalin mutane 130 da suka mutu a Jihar Kaduna, sakamakon wata hari da ‘yan hari da bindiga suka kai ga karamar hukumar Kajuru.

Ofisan yada labaran Jami’an tsaron Jihar, DSP Yakubu Sabo, ya gabatar da hakan ne ga hadaddiyar kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) a garin Kaduna.

DSP Sabo ya bayyana da cewa abin ya faru ne a misallin karfe bakwai na safiyar ranar Lahadi da ta gabata. “Wasu ‘yan hari da bindiga sun fada wa kauyan Barde da ke karkashin Garin Maro ta karamar Hukumar Kajuru, inda suka fada was mutanen garin da harbe-harben bindiga har sun kashe rayuka 16” inji shi.

“Hukumar mu sun bayan da ta karbi rahoton yanayin, ta watsar da jami’an tsaro a jagorancin kwamishanan hukumar na Kajuru hade da sojojin jihar don ganin cewa an kame wadanda suka aiwatar da mugun harin”

Ya kuma kara bada tabbaci da cewa hukumar su na kan bincike da magance yanayin.

Kwamishanan jami’an tsaron Jihar, Mista Ahmad Abdurrahman, ya rantse da cewa sai ya kai ga ganin cewa an kame wadanda suka gudanar da wannan, da kuma ganin cewa an hukumta su a kan doka.

A karshe ya isar da gaisuwan jinya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon harin.