Uncategorized
Allah Sarki, wata Mata ta gudu da barin jaririn ta kulle cikin leda
Abin takaici, wata Macce a Jihar Kaduna, ranar Asabar da ta gabata, ta gudu da barin yaron da ta haifa kulle cikin leda a bayan wata asibitin da ke a Badarawa, Jihar Kaduna.
Hukumar ‘yan tsaron Jiha ta (JTF) sun gano wani jariri kulle a cikin leda a bayar Asibitin Badarawa ta Jihar Kaduna ranar Alhamis da ya gabata a missalin karfe goma (10) na dare.
An bayyana da cewa an cinma jaririn ne cikin wata bakar leda da maman ta ajiye shi da kai waje da kuma wata sako da ta wallafa don duk wanda ya samu cintar yaron.
“Ba murna na bane da aikata irin wannan halin, ba kuwa jin dadin zucciya na ya kaini ga yin hakan ba; Tsoron Iyaye na ne ya sa na aiwatar da irin wannan halin, na barin yaron da na haifa da gudun hijira”
“ina mai rokon duk wanda ya samu cintar jaririn da yafe mani da kuma sa ni cikin addu’a” inji Matar da ta ajiye jaririn.
Malam Yusuf Abubakar, daya daga cikin ‘yan bangan yankin, ya bayyana da cewa sun cinma jaririn ne a bayan ginin missalin karfe goma na daren ranar Alhamis da ta gabata.
“Wasu masu adalci da hali ta gari ne suka gane da jaririn, da ganin hakan kuma sai suka yi kira ga ‘yan kungiyar mu da cewa sun gano wani abu na motsi cikin bakin leda. Muna jin hakan kuma, sai muka hari wajen don gane ko menene” inji Yusuf.
Yusuf ya kara da cewa, “Bayan isar mu a wajen, sai muka binciki ledar, muka kuma cin ma jariri ciki da kayan sawa hade cikin ledar da wasika da muke tunanin uwar jaririn ne ta wallafa wasikar”
“Da ganin hakan, anan take sai muka sanar da Mai Anguwan shiyar, daga nan kuma sai aka aika jaririn ga Hakimin Kawo har jaririn ya kai ga Hukumar Mata da Cin Gaban Al’umma ta Jihar” inji shi.
“Ko da shike, mun gano wani Mutum da wata Mata na leken jaririn daga nesa, daga hangen mu sai suka yi wuf da gujewa, har ma da barin takalmar su a anan. Muna diban cewa wata kila suna da sanin yadda aka ajiye jaririn a wajen”
Hajiya Hafsat Baba, Kwamishanan Hukumar ci gaba da harkan Mata ta Jihar, ta bada tabbacin lamarin da kuma karban jaririn don kulawa ta gaske daga hukumar.
“Abu na gaba itace kawai mu wallafa takardu tarihi akan jaririn, mu kuma mika jaririn ga Asibiti don bincike da tabbatar da cewa bai kame da wata ciwo ko cuta” inji Hajiya Hafsat.