Connect with us

Uncategorized

Ku mayar mana da Shanayan Mu – Fulani sun gaya wa ‘Yan Sandan Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Iyalin wasu Fulani da ke zama a kauyan Kaban ta karamar hukumar Igabi a nan Jihar Kaduna, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna a jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai da Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar da taimaka masu wajen ganin cewa an mayar masu da shanayan su guda 31 da suka bata a Ofishin ‘yan sandan yankin.

Mutanen sun bayyana da cewa shanayan su ya bata ne a ofishin ‘yan sandan bayan ‘yan kwanaki da ‘yan sanda suka fada wa gidan su da kwashe masu shanaye da tumaki akan wata zargi da ake da daya daga cikin su na cewar an gane shi da wata Bindiga.

“Munyi iya kokarin mu tun lokacin da ‘yan sandan suka kwashe mana shanaye don ganin cewa mun ribato shanayan da tumakin mu kuma, amma duk a banza, duk da cewa mun kashe kudi da dama” inji Abubakar Ibrahim, daya daga cikin Fulanin.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Makiyaya sun kashe wani ASP na Jami’am ‘Yan Sanda a Jihar Delta

Abubakar ya bayyana da cewa a halin yanzu sun riga sun kashe kudi kimanin naira Miliyan N1.750 don samun yancin kwato shanayan su daga hannun ‘yan sandan, “amma duk a banza ce” inji shi.

“Yaya na da Suruki na sun binciki ‘yan sandan a ofishin su don gane dalilin da ya sa suka kwashe mana shanayan har na tsawon mako biyu. Amma ‘yan sandan sun fada mana da cewa sai mun biya kudi kimanin naira dubu N580,000 kamin su bayar da shanayan a garemu.“

“Amma, abin takaici,  a halin yanzu, mun kashe kudi kimanin naira Miliya daya da dubu dari bakwai da hamsin (N1.750) kuma sun ki su sake mana shanayan har wa yau. sun gaya mana ne kawai da cewa an kai shanayan a Abuja” inji shi.

“Muna kira ga Gwamnan Nasir El-Rufai da Kwamishanan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna da su taimaka mana wajen ganin cewa an mayar mana da shanayan mu” inji Abubakar.

Ya kara da cewa, duk da zargin da aka masa na ajiyar bindiga, ya samu ganawa da daya daga cikin ‘yan sandan, kuma dan sandan ya bashi tabbacin cewa lallai zargin ba gaskiya bane.

“Amma duk da hakan ya bukace ni da biyan sa cin hanci na naira dubu N700,000 kamin a saki shanayan. Da baya ya karbi naira dubu dari biyu (N200,000) daga gare ni, amma duk da hakan basu saki shanayan mu ba” inji shi.