Uncategorized
Yakin Rundunar Sojojin Najeriya da Boko Haram
Tsakanin shekarar 2012 har zuwa yanzun nan, Rundunar Sojojin Najeriya sun yi ta gwagwarmaya da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihohin kasar Najeriya, musanman Arewacin kasar.
Yawancin mutane sun rasa Iyalan su, wasu sun rasa kayan zaman su, wasu gidaje, wasu ‘yan uwan su sun bata ba tare da kara ganawa da su ba, wasu kuma sunyi gudun hijira.
Duk da kokari da kuma barazanar da Rundunar Sojojin da kuma sauran hukumomin tsaron kasar ke yi na cin nasara ga ‘yan ta’addan; yaduwa kawai suke tayi.
Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa ‘Yan Hari sun kashe wani Kwamandan Sojojin Najeriya a Jihar Bauchi.
Mun gane da cewa duk da kokarin da Sojojin kasar ke yi, harwayau ‘yan ta’addan basu bar hare-haren su ba, amma akwai alamar cewa harin ya dan rage kadan bisa ga da.
A baya a wata sanarwa, an gano wani Soja da ba a gabatar da sunan sa ba yayi gwagwarmayan ribato ran wata karamar ‘yar yarinya daga harin Boko Haram a Arewacin kasar Najeriya.
Bisa bincike da kuma yadda aka bayar, an gane da cewa ‘yar yarinyar ta rasa Iyayen ta ne ga wata hari da ganawar wuta tsakanin Rundunar Sojojin Najeriya da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin kwanakin baya.
Wannan daya ne daga cikin nasarar da Rundunar Sojojin Najeriya suka yi a kan ‘yan ta’addan Boko Haram a tun lokacin da suka fara yaki da ‘yan ta’addan.
Ga wata hoto nan da ya nuna yada Sojan ke nuna wa ‘yar yarinyar kulawa, a yayin da yake yi mata wanka.
Wannan abin ya faru ne shekarar da ta gabata a Jihar Ebonyi.
Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari sun sace wani Firist na Katolika a Jihar Kaduna