Connect with us

Uncategorized

Hukumar INEC ta gabatar da sabon Gwamnan Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa, INEC ta gabatar da dan takaran kujeran Gwamnan Jihar Adamawa daga jam’iyyar PDP, Hon. Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin mai nasara ga tseren zaben Gwamnan Jihar da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

INEC a jagorancin Babban Malamin Zaben da ke wakilcin zaben Jihar, Farfesa Andrew Haruna ya gabatar ne da cewa Fintiri ya lashe tseren zaben ne da yawar kuri’u 376,552 fiye da dan adawan sa daga Jam’iyyar APC, Mohammed Jibrila Bindow mai yawar kuri’u 336,386 kasa da kuri’un Fintiri.

Naija News Hausa na da sanin cewa Bindow ne Gwamnan da ke kan jagorancin Jihar kamin wannan hidimar zaben da Fintiri ya lashe, aka kumar gabatar da shi mai nasara ga zaben bisa yawar kuri’u.

A tseren zaben kujerar Gwamna, Dan takara daga Jam’iyyar ADC, Sanata Abdulazeez Nyako ya zo na ukku ga zaben da yawar kuri’u 113,237, shi kuma Emmanuel Bello, dan takara daga Jam’iyyar SDP ya zo na hudu ga tseren zaben da yawar kuri’u 29792.

Mun ruwaito a baya da cewa Hukumar INEC ta gabatar da ranar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, Gwamnan Jihar Jigawa, ya nada wata sabuwar kwamiti na samar bincike ga biyar kankanin albashin ma’aikatan Jihar.

Gwamnan ya kafa kwamitin rukunin mutane goma sha biyar ne a ganewar Naija News don samar da yadda Jihar zata samu biyar kankanin albashin ma’aikata a sauwake.