Connect with us

Labaran Najeriya

Kotu ta gabatar da kame shugaban ‘yan Biafra, Nnamdi Kanu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Alhamis, 28 ga watan Maris 2019, Kotun Koli ta Abuja, babban birnin tarayyar kasa ta gabatar da kame Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘yan iyamirai Najeriya (IPOB).

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Nnamdi Kanu yayi ta barazana da kuma bugun gaba da cewa ba shugaba Muhammadu Buhari ne ke kan shugabancin kasar Najeriya ba, da cewa an musanya shi da wani mai suna Jibril daga kasar Sudan.

A baya kuma Kanu kara gabatar da wata hira da cewa lallai Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasar Najeriya daga jam’iyyar PDP ba asalin dan Najeriya ba ne.

A yau Alhamis, Alkali Binta Nyako ta gabatar a Kotun Koli da ke birnin Abuja da bukatan a kame Nnamdi Kanu akan rashin bayyanar shi a gaban kotun don wata kara da ake yi da shi.

Naija News Hausa ta gane da cewa Malama Binta, a shekarar 2017 da ya gabata, ta bayar da beli ga Nnamdi Kanu bayan wata zargi da ake yi a kansa a wannan lokacin.