Connect with us

Uncategorized

Kash! Ruwa ya Janye wani a yayin da yaki Iyo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Kashe Yaduwar Wuta (Fire Service) ta Jihar Kano sun gabatar da gano wani dan saurayi mai shekaru 20 cikin wata korama a yayin da ruwa ya dauke shi garin Iyo.

Hukumar sun bayyana da cewa sun cinma gawar Dayyabu Kashim ne a bakin wata korama a ranar Litini, 1 ga watan Afrilu da ya gabata a kauyan Dorayi Ramin Kasa da ke a karamar hukumar Gwale.

Kakakin yada yawun hukumar Fire Service ta Jihar Kano, Mista Saidu Mohammed ya gabatar ga manema labarai da cewa lallai Dayyabu na wanka ne a rafi kamin ruwan ta janye da shi. “Dayyabu bai samu wanda ya taimaka mashi ba a lokacin da abin ya faru, kamin ko a sani, ruwar ta sha karfin sa, ba da dadewa ba sai ya mutu”

Ya kara da cewa abin ya faru ne da Dayyaba a missalin karfe biyu (2PM) na tsakar ranar Litini.

“Mu karbi wata kirar gaugawa ne daga bakin Mallam Mustapha Inusa, wani mazaunin shiyar da cewa sun gano gangar jikin Dayyabu a kan rafin”

“Da jin kirar kuma sai ma’aikatan mu suka yi wuf zuwa wajen da aka gano gawar. sun kuma iske gawar Dayyabu ne a kan ruwa”

Mista Mohammed ya karshe da cewa hukumar su ta mikar da gawar Dayyaba ga hukumar ‘yan sandan yankin Dorayi.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gobarar wuta ya kame wani Makarantar Sakandiri a Jihar Kano