Connect with us

Uncategorized

Sansanin ‘yan Bautan Kasa (NYSC) ta Jihar Sokoto ya kame da gobarar wuta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta samu sabon rahoto da cewa takardu da kayakin ‘yan bautan kasa da ke a Sansanin NYSC ta Jihar Sokoto ya kame da gobarar wuta a yau Laraba, 3 ga watan Afrilu, 2019.

Gidan labaran mu ta gane da hakan ne da cewa abin ya faru ne da safiyar yau Laraba, a yayin da wajen kwancin ‘yan bautan kasan ya kame da gobarar wuta lokacin da suke hidimar su a waje.

Ko da shike a halin yanzu ba a bayyana dalili ko sakamakon gobarar wutan ba, amma wasu na jita-jita da zaton cewa hadewar wayan wutan lantarki ne ya jawo gobarar wutan.

An bayyana da cewa wasu daga cikin ‘yan bautan kasa da ke a sansanin su yi gwagwarmaya da ganin cewa sun ribato takardu da wasu kayakin su da ke cikin gidan kwancin, amma basu samu nasara da hakan ba saboda azabar wutan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wata Yarinya mai suna Ummie ta mutu a hadarin mota a yayin da take hanyar zuwa wajen hidimar bautan kasa (NYSC) a Jihar Kaduna.

Bisa bincike, babu mutum ko daya da ya mutu ko samun wata rauni a gobarar wutan. Iya dai sun rasa kayakin su da dama. Ana kan bincike da wannan al’amarin. Idan akwai wata bayani da ya biyo a baya, zamu sanar a shafin mu ta Hausa.NaijaNews.Com