Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi sabuwar Tafiya zuwa kasar Dubai

Published

on

at

An gabatar a yau da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Dubai don halartan wata zaman tattaunawa akan tattalin arzikin kasa da za a yi a kasar Jordan da kuma ta kasar Dubai.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da shugabancin kasar tayi a shafin nishadarwa ta Twitter da cewa wasu daga cikin Manyan shugabannan Jihohin kasar zasu mara wa shugaba Buhari baya zuwa hidimar.

An gabatar a sanarwan da cewa, Gwamnan Jihar Jigawa,  Abubakar Badaru da Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi tare da Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zasu bi shugaban zuwan wajen tattaunawar.

Zaman tattaunawar zai halarci wasu shugabanan kasar kuma kamar; Ministan Hidimar Kasar Waje, Geoffrey Onyeama; da Mai bada shawara ga lamarin tsaron kasar, Maj. Gen. Mohammed Babagana Monguno (rtd), tare da wasu da ba a ambaci sunan sa ba.

Zaman tattaunawar bisa sanarwa zai kasance ne daga ranar 8 zuwa 10 ga Watan Afrilu 2019, inda shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata gabatarwa.

Ga sanarwan kamar yadda aka bayar a layin Twitter;

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Senegal don hidimar nadin sabon shugaban kasar.