Connect with us

Uncategorized

Wani Matashi mai shekaru 25 ya Nutsa a ruwa dam ta Jihar Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an tsaron Jihar Jigawa sun gabatar da wani matashi da ya nutsa a ruwa a kauyan Shaiskawa da ke a karamar hukumar Kazaure.

“Dan shekara 25, Abubakar Lawan daga kauyan Shaiskawa ta karamar hukumar Kazaure ya nutsa a ruwa a ranar Laraba da ta gabata”

Hukumar ta bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Alhamis da ta wuce daga bakin Kakakin yada yawun hukuar, SP Abdu Jinjiri da cewa abin ya faru ne a missalin karfe shidda na maraicen ranar Laraba.

SP Abdu ya bayyana da cewa Abubakar ya fada ne cikin DAM din a yayain da Hukumar Yaki da Amfani da Mugan Kwayoyi (NDLEA) ke bin shi da kamewa bayan da aka gane shi da alamun ajiyar mugan kwayoyi.

“Ganin wananan ne wasu Matasan yankin suka fusata da kone Ofishin Hukumar NDLEA da ke a yankin” inji Jinjiri.

“Mun karbi kirar gaugawa daga Ofishin mu da cewa wasu Matasa sun haska wa Ofishin Hukumar NDLEA a wuta. Anan take Jami’an tsaro suka hari wajen don dakatar da yaduwar wuta.”

Ko da shike Jinjiri ya bayar da cewa matasan sun yi wa daya daga cikin Ofisoshin hukumar rauniuka da dama.

“Wutan bai kone Ofishin ba duka, amma ya kame gefen Ofishin ta bangare daya”

Jinjiri ya bayyana da cewa Jami’an tsaro na kan bincike akan lamarin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Kashe Yaduwar Wuta (Fire Service) ta Jihar Kano sun gabatar da gano wani dan saurayi mai shekaru 20 cikin wata korama  inda ya nutsa a ruwa a yayin da ya ke Iyo.

Hukumar sun bayyana da cewa sun cinma gawar Dayyabu Kashim ne a bakin wata korama a ranar Litini, 1 ga watan Afrilu da ya gabata a kauyan Dorayi Ramin Kasa da ke a karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano.