Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Baban Leah Sharibu ya kamu da Ciwon bugun Jini

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Uban Leah Sharibu, daya daga cikin yaran makarantar Dapchi da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a baya, ya kamu da ciwon bugun jini.

Naija News Hausa ta gane da wannan rahoton ne a yayin da wakilan yankin Chibok da Dapchi suka gabatar a ziyarar su ga Annabi Temitope Joshua da aka fi sani da suna TB Joshua, shugaban wata babban Ikklisiya ta Jihar Legas da aka fi sani da ‘Synagogue Church of All Nations’.

Bisa ga labarai, Wakilan sun ziyarci Ikklisiyar ne da ke a shiyar Ikotun-Egbe, ta Jihar Legas a ranar Lahadi da ta gabata don bukatar addu’a da neman sakin Leah Sharibu hade da sauran ‘yan mata da ‘yan ta’addan suka sace a baya.

“Mun yi iya kokarin mu, mun kai ga karshen karfi da ganewan mu akan wannan al’amaru. Mun zo ne don bukatar addu’a daga gareka don ganin cewa an saki Leah hade da sauran ‘yan mata da aka sace su tare a kwanakin baya. mun sha kallon sujadar Ikklisiyar nan da kuma ganin ire-iren ayukan al’ajabi da ke faruwa da kuma warkas wa a wannan masujadan.” inji bayanin Wakilan da suka ziyarci T.B Joshua.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa tsohon yarinyar da ke a kangin ‘yan Boko Haram, Mista Nathaniel Sharibu ya fada da cewa yana ganin diyar shi a mafarki kusan kullum.

Mun tuna da cewa Leah Sharibu na daya daga cikin ‘yan makaranta da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kwashe daga Makarantar Sakandiri na Mata na garin Dapchi ta Jihar Yobe kwanakin baya.