Connect with us

Uncategorized

Kalli bayanin Farfesa Attahiru Jega akan Hidimar Zaben 2019

Published

on

at

Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC), ya gabatar da wata zargi akan Lektarorin Manyar Makarantar Jami’ar Kasa.

“Yan Siyasa sun ci zarafin wasu manyan Laktarorin makarantun Jami’a don kadamar da makirci a zaben da aka kamala a kasar makonnai da suka gabata.” inji Jega.

Farfesa Jega ya gabatar da zargin ne a wata zaman tattaunawa da ya halarta a Makarantar Jami’ar ‘Bayero University Kano (BUK)’, inda Jega ya zargi ‘yan takara ga zaben shekarar 2019 da yin amfani da laktarorin makarantun jami’a don gudanar da makirci a hidimar zabe, musanman a Jihar Kano, inji shi.

“Malaman Makarantar BUK da suka bayar da kansu ga ‘yan siyasa don kadamar da makirci da halin cin hanci da rashawa a hidimar zaben kasar sun kada girman su, sun kuma karya dokar hidimar zaben kasa”

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Farfesa Attahiru Jega ne tsohon shugaban Hukumar INEC, shi ne kuma ya gudanar da hidimar zaben 2015 da aka bada tabbacin cewa zaben shekarar 2015 ta kasance fiyayyen zabe mafi haske da daraja a kasar Najeriya.

“A ganewa na, na kula da cewa matsalar da kasar mu ta Najeriya ke fuskanta ya kasance ne sakamakon yadda aka kada darajan dimokradiyya a kasar, musanman yadda masu karfi suka raunana hidimar zaben kasar” inji Jega.

“Ku diba abin da ya faru a zaben da aka karshe a yankuna hudu ta BUK, zaben ya kasance da rashin haske bisa makircin da aka kadamar a zaben”

Ya bayyana da cewa ‘Yan Siyasa sun hada kai da Laktarorin Makarantun Jami’a da suka yi aikin Malaman zabe don kadamar da halin da ya karya dokan zaben kasar.

“Wannan matakin nasu itace dalili da sakamakon matsalar shugabanci da kasar Najeriya ke fuskanta” inji Jega

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Gudanar da Zaben Jihar Zamfara (ZASIEC) ta gabatar da ranar da za a kadamar da zaben Kansilolin Jihar Zamfara.