Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 24 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 24 ga Watan Afrilu, 2019
1. Yadda Obasanjo ya taimaka wajen kafa Kungiyar Boko Haram – Soyinka
Kwararre da kuma Shahararren Marubicin Littafai a Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya zargi Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo da taimakawa wajen kafa Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Soyinka ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da ya bayar ga BBC, da cewa Obasanjo na da hannu ga kafuwar kungiyar ta’addancin a yayin da ya kasa dakatar da wani Gwamna a Arewacin kasar daga kafa wata rukuni da ya kira “theocratic state.”
2. Shugaba Buhari yayi bayani game da kashe-kashen da ke aukuwa a Jihar Gombe
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin sa da nuna bacin rai akan kashe-kashe rayukan Kiristoci da aka yi a Gombe a ranar hidimar Bikin Easter da ta gabata.
Buhari ya bayyana abin a matsayin abin kaito, ya kuma yi gaisuwar musanman ta ta’aziyya ga Iyalan mutanen da aka kashe a harin.
3. Zaben Jihar Osun: PDP sun ki amince da kasancewar Alkali Oyewole cikin rukunin Shari’ar karar
Kwamitin Kadamarwa ta Tarayyar Jam’iyyar PDP ta bayyana rashin amincewa da kasancewar Alkali J.O.K. Oyewole cikin mamban masu shari’a akan karar zaben Jihar Osun da ake yi.
PDP sun nuna hakan ne da zargin cewa Oyewole na da liki da shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya, Bola Tinubu, sabili da hakan, a iya kadamar da makirci, a bayanin su.
4. Zaben Legas: Ina da tabbaci ga Nasaran karar zaben Legas – inji Sanwo-Olu
Dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Legas daga Jam’iyyar APC a zaben 2019, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana a ranar Talata da ta wuce da cewa yana da tabbaci ga cin nasara ga karar da ake akan zaben Jihar Legas.
“Ina da bugun gaba da tabbacin cewa zan yi nasara ga karar da ake a Kotun Koli ta Ikeja, akan zaben ranar 9 ga watan Maris da ya gabata.” inji Shi.
5. Biafra: Nnamdi Kanu ya bayyana tabbacin cewa Buhari ba dan Najeriya ba ne
Shugaban Kungiyar Iyamirai (IPOB) da ke yaki da yancin Biafra, Nnamdi Kanu ya bada wata sabuwar tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ba dan Najeriya ba ne.
A bayanin shi a gidan Radiyon Biafra a karshen makon da ta gabata, Nnamdi Kanu ya ce “Da Mataccen Muhammadu Buhari, da kuma Jibril al Sudani da aka yi munsayan shugaban da shi, duk ba ‘yan Najeriya ba ne.”
6. Buhari da Sarkin Qatar sun yi wata ganawar kofa kulle
A ranar Talata da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari yayi zaman tattaunawa da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hammad Al-Thani, a nan cikin fadar shugaban kasa.
Tattaunawar ya fara ne bayan isowar Sheik Tamim a missalin karfe 12:15 na ranar Talata da ta gabata.
7. Masu Adalci kawai ne Buhari ke bukata a cikin Rukunin shugabancin sa – APC
Naija News ta gane da cewa Kwamitin Kadamarwa ta Tarayyar APC na kokarin ganin cewa masu adalci ne kawai zasu kasance a cikin rukunin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin shi na karo biyu.
Akwai ganewa da cewa shugaba Buhari zai shiga shugabancin ta karo biyu ne a kasar daga ranar 29 ga watan Mayu 2019, bayan an gama hidimar rantsar da shi.
8. Dogara ya mayar da martani ga Bola Tinubu akan wata zance
Kakakin yada yawun gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara yayi Izgili da kuma mayar da bakar magana ga shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya, Bola Tinubu.
A wata gabatarwa da aka bayar a bakin Mista Turaki Hassan, mataimakin yadarwa ga Dogara, ya bayyana da cewa Tinubu mutun ne mara fasaha da ganewa akan hidimar kasafin kasa.
9. Dino Melaye yayi barazanar yin karar Gwamnan Jihar Kogi
Sanatan da ke wakilci a Jihar Kogi daga gidan Majalisar Dattijai, Sanata Dino Melaye, ya gabatar da cewa zai yi karar Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi a Kotun Kara akan wata zargi.
Ya bayar da cewa zai hada hannu da Gidan Majalisar Wakilan Jihar Kogi da gabatar da kara akan Yahaya Bello.
Ka samu karin da cikakken labaran kasan Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com