Labaran Najeriya
Shugaba Buhari zai yi wata ziyarar Kai Tsaye zuwa kasar UK
Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi wata tafiyar Ziyara ta kai Tsaye zuwa kasar UK a yau Alhamis, 25 ga Watan Afrilu 2019.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da shugabancin kasar ta bayar daga bakin Mista Femi Adesina, Mataimakin shugaban kasa wajen hidimar sadarwa.
A cikin bayanin Mista Adesina a birnin Tarayyar kasar Najeriya, Abuja, ranar yau Alhamis, ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kai tsaye zuwa kasar UK bayan rabuwan sa daga Maiduguri, Jihar Borno.”
Ya kara bayyana da cewa shugaba Buhari zai komo kasar Najeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu, gabacin ranar rantsarwa ga shiga shafin shugabancin kasa ta karo na biyu.
Wannan ziyar shugaban zuwa Borno da UK ya biyo baya ne bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai a Jihar Legas, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya.
A baya, Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Tsohon Shugaban Kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya gargadi tsohon ma’ikacinsa, Reno Omokri da ya nuna halin girmamawa da tarbi’a ga shugaba Muhammadu Buhari.
Omokri ya bayyana da cewa ya karbi kira daga tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan. Ganin dalilin da ya sa Jonathan yayi kirar, Omokri ya ce “Ban taba haduwa da Fasto, Liman ko wani Fafaroma ba da irin wannan halin girmamawa irin ta Goodluck Jonathan.” inji Reno.