Uncategorized
‘Yan Shi’a sun yiwa Ofishin Gidan Majalisar Dattijai barna
Mun ruwaito a baya a Naija New Hausa, a wata sanarwa da cewa kungiyar ‘Yan Shi’a sun fada wa Ofishin gidan Majalisar Dattijai da Zanga-Zanga da bukatar Gwamnatin Tarayya da su saki Sheik Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar su.
A halin yanzu, Naija News ta samu rahoto da cewa Gidan Majalisar ta sanya masu gyara a kofar shiga Ofishin don gyara barnan da kungiyar IMN (Yan Shi’a) suka yi a lokacin da suka hari Ofishin da zanga-zanga a ranar Laraba da ta gabata.
An gano ma’aikata masu gyaran kofofi da karfuna a gaban Ofishin a yau a yayin da suke gyara gaban Ofishin.
Ka tuna da cewa Kungiyar ‘Yan Shi’a sun yi barazana a baya da cewa zasu canza rawar su idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin Sheik Ibrahim El-Zakzaky daga kulle.
Karanta wannan kuma; Wani Mutumi mai shekaru Talatin da haifuwa da suna, Uwani Danjuma ya kashe matan shi don tayi barazanar cewa zata sake Aure idan ya Mutu.