Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 2 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 2 ga Watan Mayu, 2019
1. PDP/APC: Buhari yayi karya ne da takardun WAEC na shi – inji Atiku
Dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar Adawar kasa (PDP), Atiku Abubakar Atiku Abubakar na zargin cewa karya shugaba Muhammadu Buhari ke yi game da takardun makarantar shi.
Jam’iyyar Adawar sun karyata zance da shugaba Muhammadu Buhari yayi a karar da PDP suka gabatar a kotu, inda shugaba Buhari ke fadin cewa yafi dacewa da takara bisa Atiku, musanman ga fasaha.
2. APC sun dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Segun Oni
Jam’iyyar shugabancin kasa, APC sun dakatar da Mista Segun Oni, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti da zargin cewa yana kadamar da wasu ayukan da ya karya dokar Jam’iyyar su.
Naija News Hausa ta gane da cewa APC sun dakatar da Mista Oni ne a ranar 1 ga Watan Mayu, bayan da suka gane da cewa yaki halartan kira da Jam’iyyar tayi gareshi.
3. An Sace Surukin Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Katsina
Wasu Mahara da bindiga da ba a gane da su ba sun sace Alhaji Musa Umar, Sarkin Daura, a maraicen ranar Labara da ta gabata.
Naija News ta samu ganewa da cewa ‘yan hari da makamin sun hari gidan Sarkin Daura ne a missalin karfe Bakwai na maraicen ranar Laraba, suka yi ta harbe-harbe a iska don bada tsoro ga mutane kamin suka sace Alhaji Musa.
4. Shugaba Buhari ya bada tabbaci ga Ma’aikata da cewa za a fara biyan kankanin karin albashin
Gwamnatin Tarayya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, sun bada tabbaci ga ma’aikata ga fara biyan kankanin sabon albashin Ma’aikata na naira dubu N30,000 da aka amince da ita ‘yan kwanaki da suka gabata.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a gabatarwa da shuagaba Muhammadu Buhari yayi a hidimar bikin ranar Ma’aikatan Kasar Najeriya da aka yi ranar 1 ga watan Mayu 2019, Laraba da ta wuce, a birnin Abuja.
5. Gwamnan Jihar Edo, Obaseki yayi bayani game da halakan shi da Oshiomhole
A ranar Laraba da ta gabata, Mista Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo ya karyace zance da jita-jitan da ake da cewa akwai jayayya tsakanin shi da Comrade Adams Oshiomhole, shugaban Jam’iyyar APC a hidimar neman zabe.
Obaseki ya bayyana hakan ne a saukar sa a Filin jirgin Sama ta Benin, bayan dawowan sa daga tafiyar tsawon wata daya da yayi.
6. Babu Shugaba mai Halaka ta kwarai da Ma’aikata kamar Buhari – inji Ngige
Ministan Aikace-aikacen Kasar Najeriya, Chris Ngige ya yi bayani da cewa babu shugaban kasa da ya taba halaka da ma’aikatan kasar sa kamar shugaba Muhammadu Buhari.
Ngige ya bayyana wannan zancen ne ga manema labarai a ranar Talata da ta wuce, gabadin ranar bikin Ma’aikatan kasa ta shekarar 2019.
7. Jam’iyyar ADP sun dakatar da Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar su
Kwamitin Kadamarwa na Tarayya (NWC), Action Democratic Party (ADP) sun dakatar da Yabagi Yusuf Sani, Ciyaman da kuma dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga jam’iyyar su.
Kwamitin NWC sun kuma sanya sabon Ciyaman, watau Alhaji Najeem Awodele, tsohon Ministan Harkokin Noma ta Jiha.
8. Gwamnan Ebonyi, Umahi ya tsige ma’aikata 400 hade da Kwadineta 64
Mista David Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi a ranar Laraba da ta gabata ya dakatar da ma’aikata 400 hade da wasu kwadinetoci kusan 64 a Jihar.
Naija News Hausa ta gane da cewa Gwamna Ebonyi yayi hakan ne a ranar 1 ga watan Mayu 2019.
Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com