Connect with us

Uncategorized

Kalli Ranar da Za a fara Hidimar Jarabawan Shiga Aikin Dan Sandan Najeriya ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya sun gabatar da ranar da zasu fara kadamar da jarabawan shiga aikin dan sandan Najeriya ta shekarar 2019.

Ka zamna a shirye, wata kila jarabawan bana ya zama ta Kwanfuta ko kuma na Takarda da Biro kamar yadda aka saba yi.

Kalli abubuwan da za a tafi da su da kuma Sharidun zuwa jarabawan a kasa;

  • Ana bukatar ka tafi wajen jarabawan da sakon da aka aika maka a kan waya ko ta Email na ka
  • Ana kuma bukatan ka riko wadannan Fefofin da ke a kasa; Da Original da kuma Fotokwafi

a) Guarantor’s Form (Wanda aka riga aka cika, kamar yadda aka bada sharadi akai)

b) State of Origin Certificate (Takardan Zaman dan Jiha)

c) Educational Certificates (Takardun Makarantar ka duka)

d) Birth Certificate/Declaration of Age – Takardan Haifuwa (Na Asibiti ko kuma na Kotu)
e) File na shigar da Takardu (Mai Kala)

  • Ana bukatar kuma ka riko Fasfot naka ko naki guda biyu da bai jima ba (Da sunan ka rubuce a baya da babban Harufa)
  • Ana bukatan ka bi dukan wadannan sharidu da aka bayar, rashin yin hakan na iya kada kai daga shiga Hukumar.

Jarabawan zai kumshi Shafin Fasaha, Sanin Tarihin Kasar Najeriya, hade da English Language da kuma Mathematics.

Jarabawan kamar yadda aka bayar zai fara ne daga ranar 16 ga watan Yuli ta shekarar 2019.