Labaran Nishadi
Ta’addanci: Mahara da Bindiga sun Fada wa Garin Ilo ta Jihar Kebbi da Harbe-Harbe
Naija News Hausa ta karbi rahoto cewa wasu ‘yan hari da makami, a daren ranar Litini da ta gabata sun fada kauyan Ilo, a karamar hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi da harbe-harben bindiga a iska.
Bisa bayanin mazauna kauyan, sun bayyana da cewa ‘yan harin sun shigo Ilo ne a saman babura 5 da harbe-harben harsasun bindiga a sama.
Ko da shike ba wanda ya mutu ko yi rauni sakamakon hakan, amma dai wannan ya saurata mutanen yankin gaba daya, a yayin da wasu mazauna kauyan suka yi gudun hijira zuwa kauyukan da ke a kewayan, wasu kuma suka buya a cikin daji.
Ba al’ummar kauyan kawai ba, har ma da ‘yan bangan shiyar sun tsorata da harbe-harben, ganin cewa ‘yan hari na dauke da miyagun makamai tare da su fiye da ta ‘yan banga ko wata hukumar tsaro.
A lokacin da aka tuntubi Ciyaman na karamar hukumar Bagudo, Alhaji Muhammad Kaura da bayani, ya bayyana da cewa lallai abin ya faru ne a missalin karfe 11:30 na daren ranar Litinin.
“Da farko dai an gano ‘yan harin ne da tsakar ranar cikin gari suna yawo da sayan Buredi da kayan lemun marmari da kuma ruwa. Ba wanda ya damu da karar su, har sai ga hakan” inji shi.
“A lokacin da ‘yan banga da mutanen garin suka tashi kulawa da motsin su, kwaram sai suka fito da miyagun makamai, suka kuma bi ko ta ina da harbe-harbe.” inji Kaura.
“Ganin hakan, sai mutanen gari suka fada daji da gudu don ceton rayukan su. Ko da shike ba su kashe kowa ba, ko yi wa wani rauni, ba a kuma sace kowa ba, amma sun tsorata mutane kwarai da gaske.”
A lokacin da aka karbi wannan rahoton, ba a samu karban wata bayani ba daga kakakin jami’an tsaron yankin, DSP Nafiu Abubakar, a yayin da yace zai sanar da duk abin da ya sani da harin daga baya.
Ciyaman na yankin, Muhammad Kaura, ya gargadi ‘yan banga da al’ummar Ilo da yin kokarin sanar da duk wata alamun ‘yan ta’adda da suka kula da ita a shiyar ga Jami’an tsaron don daukan matakin da ya dace a gaggauce.
KARANTA WANNAN KUMA; Takaitaccen Labarin Rayuwar Maryam Booth