Connect with us

Uncategorized

Wani Mutum mai Shekaru 40 yayi wa ‘yar Shekara 7 Fyade a Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukuma ta jefa wani mutum mai suna Sani Ibrahim a kurkuku a Jihar Katsina sakamakon zargin yi wa wata ‘yar shekaru bakwai, diyar makwabcin sa fyade.

Mutumin da aka bayyana da shekaru 40 da haihuwa, wanda zai kasance a kurkuku har zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2019, yana fuskantar hakan ne bisa zargin fyade, a karkashin Sashi na 283 na Dokar Kasa.

Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan yankin, a yayin da suke bada bayanu a kotun, sun bayyana cewa mahaifin yarinyar, Malam Hamisu Lawali ya ruwaito rahoton karar Sani ne a Ofishin su da ke a Bindawa, tun ranar 9 ga Mayu.

Da cewa Uban Yarinyar ya gabatar masu da zargin ne bayan awowi biyu da ya aka cinma makwabcin sa da yiwa diyar shi fyade a cikin gidan su.

Mai Laifin, Sani Ibrahim mazauni ne a shiyar Sabuwa Abuja Quarters, a Bindawa ta karamar hukumar Bindawa a Jihar Kano.

‘Yan Sanda sun bayyana ga Kotu da cewa a binciken su, Ibrahim yayi wa ‘yar yarinyar fyade ne har sau uku.

Ofisan ‘Yan sanda da ke gabatar da karar, Sgt. Lawal Bello, ya bayyana cewa suna kan bincike ga karar.

Alkalin da ke jagorancin karar, Hajiya Fadile Dikko ta gabatar da daga karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni, an kuma jefa Ibrahim a kurkuku har sai ga ranar.