Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 21 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 21 ga Watan Mayu, 2019

1. INEC ta janye Takaddun shaida na dawowa kan Shugabanci 25 bayan Hukuncin Kotu

Bisa umarnin da kotu ta yanke, hukumar gudanar da hidimar zaben kasar Najeriya (INEC), a ranar Litinin ta bayyana cewa ta janye takardun shaida ashirin da biyar na komawa kan shugabanci daga zaɓaɓɓun ‘yan takara ga hidimar zaben 2019 da aka kammala.

An gabatar da hakan ne daga bakin Festus Okoye, shugaban kwamitin kula Ilimin masu jefa kuri’a, a wata hidimar da aka yi a birnin Enugu ranar Litini.

2. Shugabancin Kasa sun gabatar da Ayyukan da za a gudanar a hidimar rantsar da shugaba Buhari a karo na biyu

A ranar 29 ga watan Mayu 2019, za a gudanar da hidimar rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa na Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya don shugabanci a karo na biyu a ofishin.

Hakazalika, kasar za ta gudanar da yin bikin ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar farko da kafa bikin dimokradiyya, bayan da Majalisar Dokokin Najeirya ta yanke hukunci hakan.

3. An saka Naira Marley a Kurkuku har zuwa ranar 30 ga Mayu

Alkali Nicholas Oweibo na Babban Kotun Tarayyar Legas, ya jefa Mawakin Najeriya, Naira Marley, wanda Hukumar Harkokin Kasuwancin tattalin arziki da Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) suka cafke a baya a kurkuku.

Naija News ta fahimta cewa alkalin kotun ya bada umarni hakan ne a ranar litinin da ta gabatam bayan da aka gabatar da zargi 11 da mawakin ya aikata a gabansa.

4. EFCC ta fara binciken zargi akan Rochas Okorocha

Shugaban Hukumar Tattalin Arziki da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Mista Ibrahim Magu ya bayyana cewa hukumar na kan binciken Rochas Okorocha, gwamnan Jihar Imo.

Shugaban hukumar ya gabatar da bayanin ne a lokacin da yake hira da manema labaran gidan talabijin na Channels Television a birnin London.

5. Osinbajo ya wakilci Hirar Manyan Majalisar tarayya

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci babban taron majalisar zartarwar tarayya a Fadar Gwamnatin Tarayya a Abuja.

Naija News ta samu tabbacin cewa zaman ne bisa wata rahoto da aka bayar daga bakin mai yada yawun mataimakin shugaban kasar, Mista Laoulu Akande.

6. Yan bindiga sun kai hari a Ikilisiyar ECWA, sun sace Fasto da mambobi 16

Wasu Mahara da Bindiga sun kama wani babban Fasto na Ikklisiyar ECWA, Rev. Zakariah Ido da mambobin sa 16 a Dankade ta karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

Naija News Hausa ta gane cewa ayyukan ‘yan fashi da ‘yan hari da makami na karuwa a ko yaushe a cikin jihar Kaduna da Arewacin kasar Najeriya.

7. Tattalin Arziki na Nijeriya ya karu da kashi 2.01% a cikin shafin shekarar 2019 ta farko

Yawan kudin ayyukan tattalin arzikin kasar Najeriya ya karu da kashi 2.01% a farkon kwata na 2019 idan aka kwatanta shi da karin da aka samu na 1.89% a shakarar da ta gabata.

An samu gane hakan ne bisa rahoton da hukumar ‘National Bureau of Statistics (NBS) ta gabatar.

8. Ranar 29 ga Mayu ya tabbata ranar Hutu – Lai Mohammed

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu da 12 ga watan Yuni ya tabbata ranar Hutu a kasar.

An bayyana hakan ne daga bakin Ministan Watsa Labaru da Al’adu, Lai Mohammed, a wata gabatarwa da yayi a ranar Litini da ta gabata a birnin Abuja.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com