Uncategorized
Hukumar Kwastam sun kwace Kwantenan 2 na Fatar Jaki a Legas
Jami’an Hukumar kwastam sun bayyana fata dabbobi, musanman Jakkuna a matsayin kayakin da hukuma ta hana warwashi da su don tana a karkashin kariyar fitarwa, da nufin hana dabbobi daga karewa a kasar.
Kwastam sun katange wasu babban motoci biyu da ke dauke da Kwamtena cike da Gandan Jaki da aka fi sani da suna (ponmo) a kuducin kasar Najeriya.
Bisa bayanin Hukumar Kwastam na Jihar Legas, sun bayyana da cewa Kwantena biyun da suka amshe zai kai akilla naira biliyan goma sha biyar (N15billion), idan an sayar da su.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa bayanin Kwanturola Janar na Hukumar, Aliyu Mohammed, a wata bayanin sa da manema labarai a birnin Legas.
Mista Aliyu ya bayyana da cewa sun katange motar kwamtenan ne a wani wuri da aka boye su, a yayin da ake kokarin fitar da su zuwa kasar waje.
Ko da shike Mista Aliyu bai bayyana inda hukumar suka gana da motocin ba, ya kuma yi hakan ne don kada su samu matsala tun ba a gama bincike da al’amarin ba.
“Lallai da gaske ne mun kame motoci biyu da kwamtenan Fatar Jaki cike ciki. Allah kadai ya san kimanin Jakuna da aka kashe kamin aka iya tara irin wadannan fatar har ga Kwamtena biyu” inji Aliyu.
“Ko da shike bamu samu ganawa da naman jakunan ba da aka cire fatar, ba mamaki an riga an sayar da naman jakunan ga mutane a matsayin naman saniya” inji shi.
KARANTA WANNAN KUMA; Wani ya yanke maƙogwaron abokinsa don neman sace Masa Babur