Uncategorized
Jihar Katsina ta gabatar da yin Ta’aziyya a ranar 29 ga Mayu don Mutanen da Mahara suka Kashe a Jihar
Gwamnatin Jihar Katsina a jagorancin Aminu Masari ta dakatar da duk wata hidima ta ranar 29 ga watan Mayu a Jihar, iya kawai hidimar rantsar da gwamna da mataimakin sa da za a yi a Jihar.
Naija News Hausa ta fahimta cewa gwamnatin Jihar ta gabatar da hakan ne don yin ta’aziyya ga al’ummar Jihar da aka rasa rayukan su a hare-haren da ‘yan hari da makami suka kai a Jihar a makon nan.
Sakataren tarayyar Jihar, Mustapha Inuwa, ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu da cewa lallai gwamnatin Jihar ta dauki wannan mataki ne don nuna bakin cikin su da yin ta’aziyya ga mutanen da aka kashe a Jihar.
“An gabatar da hakan ne don taya iyalan mutanen da suka mutu a hare-haren da mahara suka kawo a Jihar bakin ciki, harma ga mutanen da suka rasa abin zaman su da dabbobin su sakamakon hari” inji Inuwa.
Bisa bayanin sa, harin ‘yan ta’adda a Jihar Katsina ya kai Jihar ga rasa rayuka da dama da kuma raunuka ga wasu, harma kai wasu ga rasa gidajen su da abin rayuwa.
Inuwa a yayin da yake gabatarwan, ya gargadi al’ummar Jihar da cika da yin Addu’o’i, musanman a wannan watan Ramadana da ake a ciki don neman kwanciyar hankali da dacacciyar zamantakewa a Katsina.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa an yi hidimar addu’ar karshe ga gawakin da aka tattara sakamakon harin mahara a Jihar Katsina.
An yi hakan ne a fadar mai martaba sarkin Katsina, a jagorancin babban Limamin Masalacin Jumma’a ta Tsakar Katsina, Malam Mustapha Ahmad, kamin dada aka bizine su.