Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Shugaba Muhammadu Buhari ya Rattaba Hannu ga Kasafin Kudin Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Litini, 27 ga watan Mayu, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga takardan dokan kasafin kudin Najeriya naira Tiriliyan N8.91 na shekarar 2019, a birnin Abuja.

A ganewar Naija News, hidimar rattaba hannun ya samu halartan mambobin gidan Majalisar Dattijai har da shugaban sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki da kakakin yada yawun gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.

Ka tuna da cewa a watan Disamba ta shekarar 2018 da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kasafin kudi na naira Tiriliyan N8.83 don gabatar da shi, ko da shike, saboda hidimar Kiristimati da sabuwar shekara, Buhari bai samu ya gabatar da shi ba sai ga watan Afrilu da ta wuce.

A bayan hakan ne a ranar 30 ga watan Afrilu, gidan Majalisan Najeriya suka gabatar da amince da naira Tiriliyan N8.91 a matsayin kasafin kudin kasar ta shekarar 2019, da karin biliyan N90.3 bisa wada Buhari ya gabatar.