Uncategorized
APC ta Jihar Zamfara sun kori Marafa da wasu mutane biyu kuma
Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu daga Jam’iyyar, akan laifin makirci ga Jam’iyyar.
Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar sun kori sanatan ne da ke wakilci a Zamfara Central a gidan Majalisa ta Takwas, hade da Hon Aminu Sani Jaji da kuma Mal Ibrahim Wakkala Liman.
An sanar da korar sanatan ne a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a birnin Abuja, ranar Litini da ta wuce, daga bakin Sakataren Sadarwa na yankin, Shehu Isah.
Matakin Jam’iyyar ga dakatar da Marafa ya kasance ne bisa ga zargin cewa ‘yan siyasan sun karya dokar Jam’iyyar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawallen-Maradun ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr.
Bisa bayanin Mista Idris Yusuf Gusau, Daraktan Sadarwa ga Jihar ya bayyana cewa shanaye 750 da za a saya din za a rabar da su ne ga ragaggagu, gwamraye, yara marasa iyaye da ke a Jihar, don taimaka masu a wannan lokacin lokacin hidimar Sallah.