Labaran Najeriya
#EidAlFitr2019: Kalli Hotunan Shugaba Buhari a lokacin da ake Du’a’i a Masalacin Eid
Bayan da aka sanar a yau da tabbacin shiga watan shawwal da kuma tabbacin hidmar Sallar Eid Al Fitr ta shekarar 2019, Naija New Hausa ta gano da hoton shugaba Muhammadu Buhari tare da wasu manyan a kasar a lokacin da suke salla a masalacin Eid.
Naija News Hausa ta ci karo da hotunan ne bayan da Bashir Ahmad, mataimakin shugaba Buhari a lamarin sadarwa ta layin yanar gizo ya rabas da hotunan a shafin Twitter.
Kalli sakon da hotunan shugaba Muhammadu Buhari a kasa;
President @MBuhari attends #Eid el-Fitr Prayers earlier today at the Mabilla Barracks, in Abuja. #EidMubarak pic.twitter.com/Vw8apB0t5i
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) June 4, 2019
Shugaba Buhari yayi hidimar Sallar ne a Masalacin Eid da ke a Mabilla Barracks, anan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a yau 4 ga watan Yuni 2019.
KARANTA WANNAN KUMA; APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu kuma.