Connect with us

Labaran Najeriya

Sabuwa: Shugaba Buhari ya musanya sunan Eagles Square da suna MKO Abiola, karanta dalili

Published

on

at

advertisement

A yau Laraba, 12 ga watan Yuni 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya canza sunan Babban Filin Wasan Tarayya,  Abuja National Stadium da musanya shi da sunan tsohon shugaban kasar Najeriya, Moshoood Abiola da aka fi sani da MKO.

Ka tuna da cewa Mista Moshood Abiola ne dan takara da ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya a ranar 12 ga watan Yuni, a shekarar 1993.

A yau Laraba, shugaba Buhari a yayin da yake gabatarwa wajen hidimar Dimokradiyya da aka yi a cikin Filin wasan kwallon da ke a birnin Tarayya, Abuja, ya sanar da musanya sunan Filin kwallon da sunan Moshood Abiola.

A bayanin sa, ya ce “An dauki wannan matakin ne don tunawa da kuma girmama mai nasara ga hidimar zaben shugaban kasa ta shekarar 1993 da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘Yan Majalisar Dokoki 6 a Jihar Imo sun koma ga Jam’iyyar PDP.

‘Yan Majalisar sun gabatar ne da komawarsu ga Jam’iyyar PDP a wata wasika da suka wallafa, wadda aka karanta a bakin magatakardan gidan majalisar jihar, ranar Litini da ta wuce.