Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 13 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 13 ga Watan Yuni, 2019
1. Shugaba Muhammadu Buhari yayi gabatarwa ranar Dimokradiyya 12 ga Yuni
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 12 ga watan Yuni 2019, yayi gabatarwa na farko a sabon ranar Dimokradiyya da aka yi a Filin Eagle Square da ke a birnin Abuja.
A cikin gabatarwan shugaban, ya kafa baki ga zancen wutan lantarki, Tsaro, Tsarafa ayuka, Samar da Aiki da dadai sauransu.
2. Obasanjo, Jonathan da tsohin shugabannai a Najeriya sun yi watsi da ranar Dimokradiyya
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, hade da wasu manya a kasar Najeriya sun kauracewa da halartan hidimar sabon ranar Dimokradiyya da aka gudanar a karo ta farko, ranar 12 ga watan Yuni, 2019.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa harma da tsohin shugabannai kamar, Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar sun ki bayyana a hidimar.
3. Shugaba Buhari ya musanya sunan Filin Eagle Square da MKO Abiola
A ranar Laraba 12 ga watan Yuni da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari a hidimar sabon ranar Dimokradiyya ya canza sunan babban Filin wasannai na birnin Tarayya daga ‘Eagles Square’ zuwa sunan tsohon shugaba a Najeriya, Chief Moshood Kashimawo Olawale Abiola (GCFR), da aka fi sani da MKO Abiola.
Bisa sanarwan Buhari, Naija News Hausa ta gane da cewa sabon sunan filin a yanzu shine Moshood Abiola stadium.
4. Atiku na da daman bayyana rashin amincewa da zaben shugaban kasa ta Fabrairu – Jonathan
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya gabatar da cewa dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar na da daman karar rashin amincewa da sakamakon zaben watan Fabrairu ta shekarar 2019.
Ka tuna da cewa Hukumar INEC ta gabatar ne da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga tseren zaben shugabancin Najeriya da aka yi a watan Fabrairu.
5. Buhari yayi sabon alkawari ga Matalauta Miliyan 100 a kasar Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da yake gabatarwa ranar Laraba a hidimar Dimokradiyya, yayi sabon alkawari da cewa zai tabbatar da cewa Matalauta akalla Miliyan 100 zasu koma ga wadata a kasar Najeriya nan da shekaru goma.
Naija News Hausa ta gane da rahoton ne a bayanin Buhari a filin Eagles Square ta birnin Tarayya, watau a lokacin da yake gabatarwan ranar Dimokradiyyar Najeriya.
6. Jirgin Saman Rundunar Sojojin Sama ta kife a Jihar Katsina
Daya daga cikin Jirgin sama da Rundunar Sojojin Sama ke yawo da ita a Jihar Katsina ya rushe a yayin da suke kokarin sauka.
An bayyana hakan ne ga Naija News Hausa a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba da ta wuce, daga bakin mista Ibikunle Daramola, Daraktan yadar da labarai ga rundunar.
7. Bam ya fashe a wata gidan kasuwanci da ke a Port Harcourt
Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa anyi wata mumunar tashin Bam a wata gidan kasuwanci da ke a birnin Port Harcourt ta Jihar Rivers, da dauke rayuwa bayan mutane da dama sun yi raunuka.
Abin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata, a missalin karfe biyar na maraice.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com