Uncategorized
Mahara da Bindiga sun sace Matan Ciyaman na Kungiyar Ma’aikata a Jihar Taraba
Naija News Hausa, kamar yadda aka bayar a rahotannai da cewa wasu ‘yan hari da makami a daren ranar Alhamis da ta wuce sun sace malama Abigail Gambo, matan shugaban kungiyar ma’aikatan Najeriya (NLC) na Jihar Taraba.
Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, DSP David Misal ya bayyana a rahoto da cewa maharan sun sace matan Mista Peter Gambo, ciyaman na kungiyar ma’aikatan jihar Taraba (NLC) tare da Mista Mista Emeka Okoronkwo, shugaba da jagoran kamfanin Our Nation Bread company.
“An sace su biyun ne a gidajensu da ke a shiyar Magami, nan a Jalingo, a missalin karfe daya (1:00 am) na safiyar ranar Alhamis da ta gabata” inji shi.
“Lallai hakan ya faru, sun sace mutum biyu ne da kuma yiwa mutun daya rauni a safiyar ranar Alhamis a birnin Jalingo.”
A yayin da ake bada tabbaci ga lamarin, Mista Gambo, mijin matan da aka sace ya fada da cewa, “Sun sace mata na ne, suka kuma tafi da ita a inda ba wanda ya san dashi. Na riga na sanar da hakan ga Jami’an tsaro da al’amarin” inji shi.
Ya kara da cewa har yanzu maharan basu kira shi ko kuma wani ba game da biyan kudi ko daukan wani matakin kwato yancin su.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Mista Okoronkwo, watau jagoran kamfanin ‘Our Nations Bread Bakery’ da aka sace tare da matan Gambo makwabci ne a unguwa guda.
An kuma bayar a rahoto da cewa ‘yan hari da makamin sun harbe mai gadin gidan Mista Okoronkwo a kafa a yayin da suke kokarin sace maigidansa.
KARANTA WANNAN KUMA; Hukumar JAMB ta gabatar da lambar maki da Jami’o’i zasu karba ga neman shiga makaranta a shekarar 2019.