Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 17 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 17 ga Watan Yuni, 2019
1. Dole ne Buhari ya bukacemu wajen Sanya Ministoci – inji Ciyamomin APC
Ciyamomin Jam’iyyar Shugabancin kasa (APC) ta Jiha da jiha sun gargadi shugaba Muhammadu Buhari da yin kira garesu kamin kafa rukunin shugabancin sa.
Ciyamomin Jam’iyyar sun gabatar da hakan ne a wata taron Kwamitin kadamarwa ta Jam’iyyar da aka yi a birnin Abuja.
2. Atiku yayi bayani game da gudanar da zanga-zanga akan shugabancin Buhari
Dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Lahadi da ta wuce gabatar da yin watsi da jita-jitan cewa yana da shirin kadamar da Zanga-Zanga ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da hukumar INEC.
Atiku ya bayyana watsi da zancen ne a wata sako da ya wallafa a layin yanar gizon nishadarwa ta Twitter.
3. Kotun Kara ta gabatar da ranar da zata yi hukunci tsakanin Adeleke da Oyetola
Babban Kotun Shari’a ta bayar da ranar Ltini, 16 ga watan Yuni don gabatar da hukunci akan karar neman yancin kujerar mulki da Sanata Ademola Adeleke ya gabatar akan Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola.
An kuwa sanar da ranar ga Jam’iyun da shari’ar ya shafa kamin ranar hukunci ta karshe.
4. Ya kamata Buhari ya bada daman takara ga Kudu maso yammacin Najeriya a 2023 – Lawan
Shugaban Gidan Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC duka da bada daman neman takaran kujerar shugabancin Najeriya ga Kudu maso yammacin kasar a zaben shekarar 2023.
Sabon Shugaban Sanatocin Najeriya ya gabatar da hakan ne a aranar Asabar da ta wuce a yayin da yake bayani da manema labarai a birnin Yola, Adamawa.
5. Gwagwan Biri ya hadiye kudi Naira Miliyan N6.8m a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni ga hukumar bincike da cin hanci da rashawa don bincike ga Naira Miliyan Shidda da dubu dari Takwas (N6.8m) da ake zancen cewa gwagwan biri ya hadiye a gidan adana dabobin Jihar.
Naija News Hausa ta fahimta bisa sanarwa da cewa gwagwan birin ya hadiye kudin ne da aka samu daga wadanda suka ziyarci gidan kulawa da dabobin a lokacin hidimar Sallar Eid.
6. Akalla mutane 34 aka kashe a sabuwar harin mahara da bindiga a Zamfara
Rahotannai ta bayar da cewa kimanin mutane 34 ‘yan hari da makami suka kashe a wata hari da aka kai a kauyuka uku ta karamar hukumar Shinkafi, a Jihar Zamfara.
Naija News Hausa na da sanin cewa harin ya faru ne ranar Jumma’a da ta gabata a kauyukan Gidan Wawo-Katuru, Tungar Kaho-Galadi da kuma kauyan Kyalido-Katuru.
7. Shugaba Buhari ya tallafa wa Makarantun Jami’a da Naira Biliyan N208bn
Shugaba Muhammadu Buhari ya bada tallafin kudi naira biliyan N208 ga Manyan Makarantun Jami’a ta Gwamnatin Tarayyar kasa.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da shugaban yayi ranar Asabar, 15 ga watan Yuni, a hidimar murna da karshewa ga daliban jami’ar makarantan University of Abuja.
8. Tau! Ga babban Matsala a yayin da Hukumar EU suka yi karyace Atiku
Hukumar Kula da Hidimar zabe ta Turai (EU EOM), a ranar Asabar da ta wuce sun yi watsi da zancen Atiku Abubakar da cewa Hukumar INEC tayi amfani da wata Na’urar Kwamfuta don ajiye sakamakon zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Naija News ta tuna a baya da cewa Atiku Abubakar ya gabatar da cewa Hukumar INEC taki gabatar da ainihin rahoton zaben da ke a kwamfuta, akan cewa sun aikatar da makirci ga gabatar da shugaba Muhammadu Buhari ga mai nasara a hidimar zaben 2019.
9. Makarantan Soja ta NDA sun saki sunan masu nasara ga shiga Jami’ar
Babban Makarantan Sojoji ta Nigerian Defence Academy (NDA) ta saki jerin sunan mutane da suka yi nasara ga jarabawan neman shiga makarantar sojoji da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni 2019.
Bisa sanarwan da hukumar ta bayar daga bakin Rajistra na makarantar, Brig. Gen. I. M. Jallo, ya bayyana da cewa dalibai da suka yi jarabawan zasu bayyana a gaban rukunin makarantar daga ranar 22 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Agusta 2019 don gabatarwa da bincike.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com