Connect with us

Labaran Nishadi

‘Yan Hari da Bindiga sun sace Matafiya 28 a Jihar Ondo (Kalli bidiyon kan hanyar da suke aiwatar da hakan)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu ‘Yan Hari da Bindiga da har yanzu ba a gane da su ba, a ranar Talata da ta gabata sun sace kimanin mutane 28, matafiya da ke kan tafiyar a wata hanya da ke a Ado-Akure, Jihar Ondo.

Bisa rahoton da aka bayar ga Naija News Hausa, mazaunan shiyar sun bayyana da cewa ‘yan harin sun ci nasara da hakan ne bayan da suka gana da matafiya cikin motoci biyu manya, guda mai girman daukan mutane 18, dayan kuma mai kujera 9.

An bayyana da cewa yanayin lalacewar hanyar ne ya sa maharan suka sami sauki da nasarar tare motocin.

An gabatar da zargin matsalar hanyar ne a wata bidiyo da aka samar da shi a layin yanar gizon nishadi ta twitter, a tabbacin cewa domin rashin kyan hanyar, ‘yan hari da makami kan katange matafiya a kan hanyar su kuma sace mutane a kowane lokaci da suka sami damar haka.

Kalli bidiyon hanyar a kasa;