Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 12 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 12 ga Watan Yuli, 2019
1. Shugaba Buhari ya mikar da sunan Tanko a matsayin babban Alkalin Najeriya (CJN)
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sunan Tanko Mohammed ga Majalisar Dokoki don amince da shi a matsayin shugaba da babban Alkalin kotun Najeriya (CNN).
Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sako da ya wallafa ga Majalisar Dattijai, da kuma shugaban Majalisar ya karanta a ranar Alhamis da ta wuce.
2. ‘Yan Sanda sun kame mambobin ‘yan Shi’a a Jihar Legas
Farmakin tsakanin Kungiyar ci gaban Musulunci (IMN), da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, ya ci gaba da gwamnatin tarayya a ranar Alhamis.
Ka tuna da cewa ‘yan kungiyar sun hari gaban Ofishin Majalisar Dattijai da ke a birnin Abuja da bukatar a saki shugaban su, Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da ke a katangewar gwamnatin Tarayya.
3. Mun gane kuskuren mu ga hidimar zaben 2019 – INEC
Shugaban Hukumar Gudanar da Zaben kasar Najeriya (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana da cewa hukumar ta gane da kuskurenta da kuma kasawar ta ga hidimar zaben 2019 da aka kamala a baya.
Ya kara da cewa lallai zasu karu da hikima a hidimar zaben 2023 ta gaba, a yayin da zasu gyara daga matsalolin da aka samu a zaben baya.
4. Atiku Vs Buhari: An kadamar da makirci a gaba na ga zaben shugaban kasa – inji wani shaida
Yahaya Shiko, wani tsohon Major da yayi aiki da hukumar INEC a hidimar zaben 23 ga watan Fabrairu a matsayin wakilin Jam’iyyar PDP a zaben Jihar Kaduna, ya ya bayyana ga kotun kara a ranar Alhami da ta gabata da cewa an kadamar da makirci a hidimar zaben don taimakawa Jam’iyyar APC da nasara.
Shiko ya gabatar da hakan ne a yayin da Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar ke gabatar da shaidu ga Kotun neman yanci.
5. NAFDAC ta sanar da hana sayar da maganin SNIPER a kasuwa
Hukumar NAFDAC, a jagorancin Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da dokan hana sayar da maganin kashe kwari a gona ‘SNIPER’, a kasuwannai da shaguna.
An sanar da hakan ne daga bakin Darakta Janar Hukumar NAFDAC, Moji Adeyeye, a wata sanarwa da aka bayar wadda ya bayyana da cewa dokar zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satunba 2019.
6. Dalilin da ya sa yaki da Cin Hanci da Rashawa ya zan da wuya a Najeriya – Magu
Ciyaman Hukumar kare Tattalin Arzikin da yaki da cin Hanci da Rashawa a Najeriya (EFCC), Ibrahim Magu ya bayyana da cewa hukumar su na yaki da masu karfi da iko a kasar shi yasa abin ya zan masu da wuya.
Magu ya karshe da fadin cewa hukumar zata karu da karfi don yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
7. Mahara da Bindiga sun sace Magatakardan Jihar Adamawa
Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa mahara da makami sun sace babban magatakardan Jihar Adamawa.
Bisa rahoton da wani dan uwa ga wanda aka sace ya bayar ga manema labarai, ya fada da cewa an sace Mista Emmanuel ne a wata munsayar harsasu da ‘yan fashi a safiyar ranar Laraba da ta wuce a gidansa da ke a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.
Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com