Connect with us

Uncategorized

El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun Musanta zargin kashe Babban Jami’in Tsaro, DCP Umar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Cigaban Harkokin Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da Shi’a ta musanta kashe Usman Umar, Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda (DCP) da ke lura da ayyukan shiyar da aka yi zanga-zanga a ranar Litini da ta gabata a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa mambobin kungiyar Shi’a a ranar Litinin sun yi artabu da jami’an ‘yan sandan Najeriya, wanda ya haifar da kisan wani babban Jami’in tsaro, DCP Umar, hade da dan jaridar Channels, Precious Owolabi da kuma wasu ‘yan membobin IMN shida.

A yayin bayani ga manema labaran Daily Post a Abuja, Abdullahi Musa, sakataren kungiyar Ilimi ta IMN, ya bayyana musanta zargin cewa ‘yan kungiyar ne suka kone darikar ofishin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).

Ya fada da cewa zanga-zangar ta kasance cikin lumana kafin ‘yan sanda suka fito da makamai da kokarin fatattakarsu kusa da Sakatariyar Tarayyar.

“Jami’an tsaro karkashin jagorancin‘ yan sandan Najeriya sun harbe membobinmu tare da raunata wasu da dama. Ina iya tabbatar muku cewa, mun dauki gawawwakin mutane shida daga kungiyar mu da jami’an tsaro suka kashe a hargitsin” in ji Musa.

“Haka kazalika Jami’an tsaron suka kuma dauke wasu gawawwakin zuwa wuraren da ba a san dasu ba. Har yanzu ba mu da cikakken tabbacin iya mutanen da aka kashe daga membobinmu waɗanda suka fito don yin zanga-zanga a Abuja. Mun yi imanin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa kafin yau ta kare. ”

“Babu wani membanmu da ya shiga haskawa motocin da kuma Ofishin NEMA wuta kamar yadda ake zargi. Amma mun fahimta da cewa hukumomi suna ta yin iyakan kokarinsu don bata mana suna ta don samun alherin tausayawar jama’a bisa IMN da yantarwar El-Zakzaky.”

Ya karshe da cewa, “Mun fahimci cewa ‘yan sanda sun rigaya da biyan wasu kudi don shiga tsakanin membobin mu da kuma tada tanzoma a tarukanmu, don cin zarafin zaman lafiya da sunan IMN” inji shi.