Connect with us

Labaran Najeriya

‘Yan Shi’a sun gabatar da karar rashin amincewa ga matakin Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), waddae aka fi sani da lakabi da Shi’a, za ta gabatar a ranar da Alhamis (a yau) da kara don nuna rashin amincewa da matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka na dakatar da ayukan kungiyar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne daga bakin Mista Femi Falana (SAN), lauya mai kare hakkin dan Adam.

Falana ya fada wa manema labaran The Punch da cewa wasu shugabannin ‘yan Shi’ar sun bukaci kamfanin lauyarsa da ya kalubalanci umarnin kotun Koli.

Lauyan ya bayyana da cewa kungiyar zata gabatar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis.

“Manyan shugabanan kungiyar ‘yan Shi’a sun kai ga amincewa da mu akan alkawarin dakatar da zanga-zanga a birnin Abuja. Ina iya tabbatar maku da cewa a gobe Alhamis za a gabatar da zancen a Kotu.”