Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 14 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 14 ga Watan Oktoba, 2019

1. Aisha Buhari ta dawo Najeriya

Naija News na bada tabbacin cewa Uwargidan Shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta dawo kasar daga Burtaniya.

Ta dawo kasar ne kasar a ranar Lahadi, 13 ga Oktoba da ta gabata, bayan doguwar hutu da ta tafi a Burtaniya. Ta kuma isa tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe ne da karfe 4.30 na safiya ta jirgin British Airways.

2. NLC Ta Faɗawa Majalisun jihohi da shirin fuskantar Yajin Aiki

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi majalisun jihohinsu da su shirya da shiga yajin aiki daga ranar Laraba, 16 ga Oktoba.

Naija News ta bayar da rahoton cewa NLC ta gargadi majalisun jihohin ta cewa zata iya shiga yajin aiki idan ba su kai da sasantawa ba da Gwamnatin Tarayya.

3. ‘Yan ta’adda sun kai hari kan gidan Adams Oshiomhole A Benin

Wasu ‘Yan ta’adda a yammacin ranar Asabar sun kai hari a gidan Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke shugabancin kasar Najeriya.

Naija News ta karbi rahoton ne a cikin wata sanarwa da aka bayar ta hannun kakakin yada yawun Ciyaman na jam’iyyar APC na kasa, Simon Egbebulam.

4. Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi ya Tsige wani Wakili

Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano ya ba da umarnin a tsige Maja Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu.

Naija News ta fahimci cewa sarkin ya tsige Maja Sidden Sarkin Kano ne, wanda ke kula da yin ado da dokin Sarkin, da cewa ya bar fadar nasa bayan shekaru 30 da aiki a fadar.

5. Dalilin da yasa Na bar Najeriya da tsawon watanni biyu – Aisha Buhari

A’isha Buhari, matar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ta karyata duk wata tsaguwa ko rashin jituwa tsakaninta da mijinta.

Uwargidan shugaban Najeriyar ta musanta jita-jitar da ke nuni da cewa akwai sabani tsakanin ta da Shugaba Buhari, da cewa rashin jituwar ne ya kai sanadiyar barinta kasar da tsawon mako biyu.

6. Sojojin Najeriya Sun Yi Magana kan Kawar Boko Haram A cikin mintina 15

Rundunar Sojojin Najeriya sun ce za su iya kawar da ‘yan ta’addan Boko Haram kai tsaye a cikin ‘yan mintina 15 na mummunan hari.

Sojojin Najeriyar sun jaddada cewa sojoji za su iya cimma wannan nasarar ne kawai idan aka samar masu da kayan aikin yadda ake bukata don magance ta’adanci a kasar.

7. APC zata Lashe Zaben Jihar Bayelsa – Lyon

Dan takarar gwamna a jihar Bayelsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Lyon, ya bayyana cewa jam’iyyarsa zata lashe zaben ranar 16 ga Nuwamba a sauwake.

Lyon yana mai da martani ne kan ikirarin da Gwamna Seriake Dickson ya yi na cewa APC ba ta da hurumi a jihar Bayelsa.

8. Dakarun Sojojin Najeriya Sun Kashe Wani Shugaban ‘Yan Fashi da Bindiga, Sarki, 59 da kuma hadi da Wasu

Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga 60, da suka hada da shugaban rundunar nan da aka fi sani da suna’Emperor.’

Wannan nasarar ya samu ne ga Sojojin ta Operation HADARIN DAJI (OPHD), inda suka kashe barayin ne a kokarin da suke zagayen kawar da masu aikata mumunar hare-hare a jihar Zamfara.

Karanta kari da cikkaken Labaran Najeriya a Naija News Hausa