Shugaba Buhari ya Nada wa Matarsa Aisha Buhari Mataimaka 6 ga Ayukanta | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Shugaba Buhari ya Nada wa Matarsa Aisha Buhari Mataimaka 6 ga Ayukanta

Published

Naija News Hausa ta fahimta bisa rahoton Mai magana da yawun ofishin, Suleiman Haruna, da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakan musanman shidda ga Uwargidansa, Aisha Buhari.

Wannan ya biyo ne bayam wata jita-jita da ya mamaye layin yanar gizo da gidan labarai da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na Shirin Karin Aure.

Kalli Jerin Mataimakan Musanman da aka amincewa Aisha Buhari a kasa;

1. Dr. Mairo Almakura – Mataimaki na Musamman kan Ofishin Hadin gwiwar Matan Shugaban Kasa (AFLPM)

2. Muhammed Albishir – Mataimaki na Musamman a Kungiyar Hadin Kan Matakan Shugabanan Kasar Afirka (OAFLAD)

3. Wole Aboderin – Mataimaki na Musamman kan kungiyoyi masu zaman kansu

4. Barr. Aiyu Abdullahi – Mataimaki na Musamman kan harkar yada labarai da Sadarwa

5. Zainab Kazeem – Mataimaki na Musamman kan al’amuran cikin gida da zamantakewa

6. Funke Adesiyan – Mataimaki na sirri akan Abubuwan cikin gida da kuma zamantakewa

Naija News Hausa ta fahimta da cewa wadannan mataimakan zasu fara ayukan su ne a gaggauce ba tare da wata jinkiri ba.

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].