Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 25 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 25 ga Watan Oktoba, 2019

1. Najeriya Yanzu Tana lamba na 131 a layin Saukin Kasuwanci da Babban Bankin Duniya

Najeriya ta taka rawar gani a sabon tsarin rahoton harkokin kasuwancin da bankin duniya ta fitar na hawa sama da tsani 15 daga matsayinta a 2019.

Dangane da rahoton shekarar 2020 da Bankin Duniya ta fitar a ranar Alhamis, Najeriya yanzu ta hau sama da matsayi na 131.

2. Deji Adeyanju ya Kalubalanci EFCC game da Motar Kudi da Tinubu sha Shigar a Gidansa ranar Zabe

Jagoran ‘Concerned Nigerians’, Deji Adeyanju, a ranar Alhamis da ta gabata, ya bayyana cewa ya dauki matakin kalubalantar Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) akan shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu.

Dan yaki da hakin Dan Adam, Deji ya bayyana hakan ne a shafin Facebook cewa zai gabatar da sammacin a ranar Juma’a.

3. Kotu ta dage karar Naira Marley yayin da Lauyoyi suka fara gwagwarmaya kan kujerun zama

Kotun Tarayya da ke Legas ta sake daga shigar da karar da ake wa mawaki, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da lakabi Naira Marley.

Naija News ta fahimta da cewa takaddama ta barke ne tsakanin Mista Rotimi Oyedepo, mashawarcin Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) da kuma lauyan Naira Marley Mista Olalekan Ojo SAN, hade da wasu manyan lauyoyi guda biyu a wannan bangaren.

4. EFCC ta Kama ‘Yahoo Boys’ 10 da ake zargi a garin Ilorin

Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da sata a layin yanar gizo a Ilorin tare da kwace wasu kayayyaki masu hadari, Magunguna da kudaden karya daga hannunsu.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, hukumar EFCC da ke Ofishin su a Ilorin ta bayar da sammacin kama matasan ne bisa laifuffukan da ake zarginsu da su da suke da alaka da yaudarar yanar gizo da sauran laifukan da suka shafi zamba.

5. Rauf Aregbesola yayi Magana kan Sakin Wasu ‘Yan Fursuna Don rage yawar ‘yan Fursuna

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce an kafa kwamiti domin ganin yadda za a iya rage yawar ‘yan fursuna a gidajen yarin da ke Najeriya a cikin watanni shida.

Wannan itace bayanin Ministan yayin da yake jawabi a wurin sauraron karar da kwamitin hadin gwiwar majalissar dokokin kasar ta shirya kan batun sanya hannu.

6. Cikakken Jawabin Shugaba Buhari A Taron Rasha

A ranar Alhamis din da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Najeriya na fatan ta rungumi sabon salo na hadin gwiwar Afirka da kasar Rasha da kuma sake farfado da dangantakar Najeriya da Rasha.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron farko na taron Rasha da Afirka.

7. NJC ta nada Sabbin Alkalan Kotun Koli hudu

Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta ba da shawarar nada sabbin alkalai hudu ga kotun kolin Najeriya.

Majalisar ta kai ga yanke wannan shawarar ne a taron da ta yi ranar Talata da Laraba da ta wuce.

8. Sojojin Najeriya sun Kama ‘Yan kungiyar Boko Haram 2

Jami’an rundunar Sojojin Najeriya sun kama wasu membobin kungiyar nan ta Boko Haram biyu wadanda suke cikin jerin sunayen da Sojojin Najeriya ke neman kamu tun da dadewa.

Naija News ta fahimci cewa an kama mambobin kungiyar ta Boko Haram ne tare da hadin gwiwar dakaru tsaro 26 na Task Force Brigade, da Civilian Joint Task Force (CJTF) da kuma Rundunar Sojojin 21 Special Armoured Brigade.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa