Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 4 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 4 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Dalilin da ya sa ya kamata ‘yan Nijeriya su hanzarta Amfani da Kayayyakin da aka kera a cikin Kasar – Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su amince da diban muhinmancin saye da amfani da kayayyaki da ake kira a kasar.

Buhari ya fadi hakan ne yayin jawabin sa na farko a yayin bude bikin gabatar da Kasuwanci na kasa da kasa a shekarar 2019 da aka yi a birnin Legas.

2. Yadda Ofishin Osinbajo ke Kuntata Mani – Obono-Obla ya gayawa Buhari

Tsohon shugaban kwamitin Bincike na Musamman na Maido da kadarorin Jama’a (SPIP), Okoi Obono-Obla ya zargi ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da tsananta masa saboda biyayya ga Shugaba Muhammadu Buhari da yake yi.

An kafa hukumar ta (SPIP) ne domin duba lamuran rashawa, cin mutuncin ofis da sauran lamuran da jami’an hukumar suka aikata.

3. Abin da rufe Bodar Najeriya ya jawowa Najeriya – Bichi

Darakta-Janar na ma’aikatar (DSS), darakta-janar, Yusuf Bichi ya bayyana fa’idar rufe bodar Najeriya da Gwamnatin kasar ta yi.

A cewar Bichi, rufewar bodar da aka yi a kasar Najeriya ya taimaka wajen dakile safarar makamai a cikin kasar.

4. Obiano Yayi Ikirarin cewa Mugayen Ruhohi Sun Mamaye gidan Gwamnatin Anambra

Willie Obiano, gwamnan jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya, ya bayyana da cewa mugayen ruhohi sun maye gidan Gwamnatin Anambra.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Obiano ya yi wannan zargin ne a ranar Asabar da ta gabata a hannun sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Solo Chukwubelu.

5. Sarkin Daura Ya Mayar da Martani Game da Dangantakar Osinbajo da Buhari

Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar ya bayyana alakar da ke tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa, Yemi Osinbajo a matsayin Alaka mafidacewa a tarihin Najeriya.

Sarkin ya sanar da hakan ne ranar Asabar yayin bikin Turbaning da aka yi wa Alhaji Musa Haro a matsayin Dan Madamin Daura.

6. ‘Yan Hari da Bindiga sun kashe Mutane biyu a Benue

Wasu Mahara da Bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Patrick Kumbul, shugaban ICT, Radio Nigeria, Harvest FM Makurdi, da kuma wani Shongo Wuester a Makurdi, jihar Benue.

Don tabbatar da kisan, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue, DSP Sewuese Anene, ya bayar da cewa an kashe mutane biyun ne a daren Asabar.

7. Obaseki Ya Mayar da Martani akan Hari da aka kai masa a Gidan Oshiomhole

Gwamna Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo ya yi Allah wadai da harin da aka kai masa a gidan Shugaban tarayyar Jam’iyyar APC na kasa baki daya, Adams Oshiomhole.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa ‘yan fashi da makami sun kai hari kan ayarin gwamna Obaseki, Mataimakin Gwamna Philip Shuaibu da kuma Sarkin Legas, Rilwan Akiolu a Iyamoh, garin Oshiomole.

8. Makiyaya Sun Tura Gargadi mai karfi Zuwa ga Gwamnonin Jihohi

Makiyaya Fulani, a karkashin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Socio-Cultural Organisation, sun ba da sanarwar gargadi ga gwamnonin Jihohin a kan wuraren kiwo (RUGA) na yankunan.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, Fulani makiyayan sun gargadi Gwamnonin Jihohin ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Bodejo ya fitar.

9. Oshiomhole Ya Roki Obaseki, Oba Na Legas Kan Hari da aka kai masu a Gidansa

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya nemi afuwar Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo; Oba Rilwan Akiolu, Oba na Legas, kuma shugabar jami’ar jihar Edo, Iyahmo, Dr. Makanjuola, kan harin da aka kai kwanan nan a kan wakilin nasu a gidansa.

Kamfanin dillancin labarai ta Naija News ta ba da rahoton cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya nemi afuwa a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar daga bakin Babban Sakataren yada labaran sa, Simon Ebegbulem.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa