Connect with us

Uncategorized

Kogi: Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Yahaya Bello Rancen Biliyan 10b ‘Yan Kwanaki ga Zaben Jihar Kogi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Bello ya samu amincewar nera miliyan goma din da ya nema daga gwamnatin tarayyar kasa.

Shugaban Majalisar Dattawar, Mista Ahmed Lawan a yayin magana game da rancen kudin da aka baiwa Bello, ya bayyana cewa ya zama dole a saki kudin kamar yadda Gwamnan ya nema saboda an yi jinkirta da bashi kudin da tsawon lokaci.

Ko da shike amincewar da Majalisar Dattawa ta yi ya gamu da adawa daga Sanatocin bangaren jam’iyyar PDP. Sanatocin sun kalubalanci shugaban majalisar game da lokacin da aka amince da bada rancen.

Jagoran gidan majalisar marasa rinjaye, Sanata Enyinaya Abaribe wanda ya yi magana a madadin ‘yan adawa, ya nemi majalisar dattijai da ta kara jinkirtar amincewa da bayar da aron har zuwa mako mai zuwa.

Naija News Hausa ta kula da cewa Enyinaya ya fadi hakan ne da ganin cewa zaben Gwamna a Jihar Kogi ya gabata da ‘yan kwanaki Uku kawai, wata kila jam’iyyar adawar na tuhumar cewa za a yi amfani da kudin ne don neman zabe da gudanar da makirci ko neman kuri’a.

Ko da shike dai wannan kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta fahimci cewa rancen asalinta an gabatar da shi ne da sunan magance basussukan da ke a kan gwamnatin jihar Kogi, sakamakon ayyukan da aka aiwatar a madadin Gwamnatin Tarayyar kasar.