Uncategorized
APC/PDP: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Fada Kan Kayakin Zabe a Jihar Bayelsa
Fada ya Tashi a Yayin Hidimar Zaben Gwamna a Jihar Bayelsa
Masu fafutukar siyasa sun yi karo da juna game da yadda za a samar da kayayyakin zabe zuwa rumfunan zabe a Otueke, karamar hukumar Ngbia na jihar Bayelsa.
Naija News ta ba da rahoton cewa lamarin ya faru ne a Cibiyar Rajista ta INEC (RAC) a cikin Makarantar Sakandaren Unguwar Otueke da karfe 10.45 na safe inda ‘yan tawayen da ke dauke da makamai suka watsar da ‘yan jaridu da masu sa ido kan zaben.
Matasan sun tayar da fada ne a yayin gardama da rashin jituwa game da inda za a kai wasu kayan zaben.
Wani jami’i da kuma ma’aikacin hukumar INEC, wanda ya zanta da ‘yan jaridar The Punch ya danganta rade-radin rarraba kayayyakin zaben akan tsanancin wasu matasa a cikin yankin.
“Ku zargi matasan yankin da jinkiri da sakaci wajen rarraba kayan zaben. Kayakin zaben sun isa runfar zabe ne da misalin karfe 11:30 na safe bisa agogo, amma matasan yankin sun nace kada mu tafi da kayaki.”