Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba, 2019

1. 2023: Tinubu Ya Dace da Zaman Shugaban Kasa – Guru Maharaj Ji

Wanda ya kafa kungiyar ‘One Love Family’, mai suna Satguru Maharaj Ji, ya ce shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya cancanci zama shugaban kasa a 2023.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake Magana a wani taron tattaunawa da aka gudanar a kauyen Maharaj Ji.

2. Sagay ya Tabbatar da Kama Tsohon Babban Janara, Adoke

Shugaban kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, ya tabbatar da kama tsohon babban Janarar Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Mohammed Adoke.

Sagay ya tabbatar da kamun ne yayin wata ziyarar girmamawa a hedikwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a jiya, 20 ga Nuwamba.

3. EFCC ta gurfanar da Maina a gaban Kotu saboda tuhumar da ake masa

A ranar Laraba da ta wuce ne aka gurfanar da Abdulrasheed Maina a gaban Mai shari’a Abubakar Kutigi na Babbar Kotun FCT da ke Gwagwalada kan tuhumar da ake masa na satar fasaha.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da Maina ne akan tuhume-tuhume tara da ake zargi da badakalar cin hancin na Miliyan N738.6m.

4. Jam’iyyar APC ta tura Manyan Wakilai Zuwa Jihar Edo

Jagorancin jam’iyyar APC na kasa ta tura wata tawaga mai cikakken iko don shawo kan rikice-rikicen da ke afkuwa a jam’iyyar anan jihar Edo.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo na munsayar yawu tun da dadewa.

5. Kogi: Dino Melaye Ya Hari Ofishin INEC Da Faifan Bidiyo 21 Don Neman Soke Zabe

Sanatan da aka kora kwanan nan mai wakiltar mazabar Kogi West Senatorial, Dino Melaye, a yau ya ziyarci hedikwatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) don neman a soke zaben ranar 16 ga Nuwamba a gundumar.

Dino a isarsa Ofishin ya samu marabta daga hannun Sakataren INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishina na kasa / Shugaban Kwamitin yada labarai da kwamitocin Ilimin masu jefa kuri’a, Festus Okoye.

6. Kudurin Dokar Shafin Sadarwa ta Yanar Gizo ya Bayyana a Majalisar Dattawa a karo Ta Biyu

Dokar kafofin watsa labaru da Sadarwa a ranar Laraba ya sake bayyana a karatu na biyu a cikin Majalisar Dattawa. Ana sa ran dokar za ta hana yin karya kan yanar gizo ga ‘yan Najeriya idan har aka sanya su cikin doka.

Sanata mai wakiltar Mazabar Gabas ta Tsakiyar Jihar Neja, Musa Mohammed Sani, shine ya gabatar da kudirin a Majalisar kasa.

7. Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar zartarwa 009

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan Dokar zartarwa ta 009 don kawo karshen matsalar kashi a fili a Najeriya a shekarar 2025.

Sabuwar dokar da Buhari ya sanyawa hannu ta ce, “A ganin wannan dokar, Ana hangen Najeriya da fita tsarin kasashe da ake kashi a fili daga nan har zuwa 2025.

8. Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Cika Shekaru 62, Ga Sakon Shugaba Buhari Zuwa Gareshi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murna a cikar shekara 62 ga haihuwarsa ta.

Buhari ya taya Jonathan murna ne ta hanyar hada kai da ‘yan kasar da yin addu’o’in tsawon rai, lafiya da kuma karin karfin gwiwa don ci gaba da yiwa kasa hidima.

9. Kotu Ta Dakatar da ‘Yan Majalisar PDP Biyu a Kaduna, Ta Bada Umarnin Sake Zabe

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a jihar Kaduna ta sallami wasu mambobi biyu a majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata.

‘Yan Majalisa biyun suna wakilci yankin Kagarko da Sanga bi ne a majalissar dokokin jihar Kaduna.

Naija News ta fahimci sunan ‘yan majalisa biyun da a kora da, Mista Morondia Tanko mai wakiltar mazabar Kagarko da Malama Confort Amwe na mazabar Sanga duka biyu a dandalin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa