Connect with us

Uncategorized

Sakon PDP Ga Atiku A Yayin Da Yake Murnan Cika Shekaru 73 Ga Haifuwa

Published

on

at

advertisement

Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta aikar da sakon tayin murna ga dan takarar shugaban kasa na 2019, Atiku Abubakar, yayin da yake murnar cikar sa shekaru 73 a duniya.

Babbar jam’iyyar adawar kasar ta dauki shafin nishadantarwanta na Twitter don wallafa sakon murnar ga tsohon mataimakin shugaban kasar.

Sakon na PDP na kamar haka;

“Muna taya tsohon VP na Najeriya da kuma dan takarar shugaban kasa @OfficialPDPNig murna a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019, zaben shugaban kasa, H. E. @atiku, a yayin bikin cikar sa shekaru 73 da haihuwa. Muna maka fatan alkhairi, karin lafiya da shekaru masu yawa na hidimtawa kasarmu. Barka da ranar haihuwa, Sir ”.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa wasu sanannun mutane a kasar sun aika da sakon tayin murnarsu ga dan siyasar.

Ka tuna da cewa Naija News ta ruwaito da cewa Mataimakin Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi ya taya Atiku Abubakar murna da cikar sa shekara 73 da haihuwa.