Connect with us

Labaran Najeriya

Ga Sakon Aisha, Uwargidan Shugaba Buhari A Yayin Taya Shi Murnan Cika Shekara 77

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta aika wa mijinta da sakon taya shi murnar cikar sa shekaru 77 da haihuwa.

A yau Talata, 17 ga watan Disamba 2019, Shugaba Buhari, wanda ya kwashe shekaru hudu da rabi a kan mulki a matsayin Shugaban kasa a tsarin dimokiradiyya, ya cika shekara 77.

Naija News Hausa ta fahimci cewa Aisha ta yi amfani da taken ‘Janar Muhammadu Buhari’ ga mijinta.

Ka tuna da cewa kamfanin dilanci labarai ta PUNCH a cikin wata sanarwa da suka bayar a baya sun kalubalanci gwamnatin Najeriya a jagorancin shugaba Buhari, har ma suka kira shugaban a matsayin Janara bisa yadda yake tafiyar da wa’adin mulkin sa a wannan mulkin farar fula.

A cikin wata sanarwa a daren ranar Litinin, Uwargidan Shugaban kasar ta ce, “Barka da ranar haihuwa zuwa ga nawa GMB mara lalaci.”

“Ina maka fatan kariya da shiriya ta ALLAH da kuma kyakkyawan Lafiya don ci gaba da shugabancin al’amuran fadin kasarmu.”

“Tsawon Rai Ga GMB, Tsawon Rai ga Tarayyar Kasar Najeriya a baki daya.” inji sakon Aisha Buhari.