Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a 24, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 24 ga Watan Janairu, 2019
1. Kotun kara ta sanya Donald Duke a matsayin dan takaran tseren shugaban kasa na SDP
Kotun daukaka kara ta birnin Abuja ta gabatar ranar Alhamis da tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a shekarar 2019.
An koma gabatar da Donald Duke a matsayin dan takarar shugaban kasa na SDP bayan gwagwarmaya da aka yi a kotu kan matakin da aka dauka a baya na tsige Donald har da musanya shi da Farfesa Jerry Gana a ranar 14 ga Watan Disamba, 2018.
2. An gane tsohin ma’aikatan INEC da sace kudi fiye da naira miliyan dari biyu
An gano tsohin ma’aikata biyu da suka yi aiki da hukumar zabe (INEC) a Jihar Kwara da sace kudi naira dubu N264, 880,000. sunayen su na kamar haka; Christian Nwosu da Tijani.
Mun sami tabbaci da cewar Alkalin da ke gudanar da karar, ya dakatar da karar har zuwa ranar Jumma’a kamin a gabatar da hukuncin laifin su.
3. Lokaci ya kure miki da janye wa tseren takara – INEC ta gayawa Ezekwesili
Hukumar gudanar da zaben kasa INEC sun mayar da martani a kan matakin da Ezekwesili ta dauka na janye wa tseren takarar shugaban kasa ga zaben watan Fabairu da ta gabato.
A jiya Alhamis nan birnin Abuja, Sakataren Hukumar INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya gabatar da cewa basu amince da matakin ba, da cewa lokaci ya rigaya ya kure na daukar irin wannan matakin.
“Bai yiwuwa wani dan takaran shugaban kasa ya ce zai janye a wannan lokaci” inji Mista Rotimi.
4. Kotun daukaka kara ta umurci CCT ta dakatar da bincike game da karar Onnoghen
Kotun ta bada umurni da cewa a CCT da dakatar da karan babba Alkali kan zargin da ake da Alkali Walter Onnoghen, babban Kwamishinan Najeriya (CJN) don rashin gabatar da asusun kudin sa duka.
Ku tuna da cewa mai bada shawara ga CJN, Wole Olanipekun ya bukaci kotun daman ta dakatar da karar da tsawon lokatai.
5. Majalisar dattijai ta dakatar da zaman su har zuwa 19 ga watan Fabrairun, 2019
Dole ne Ƙaddamar da kasafin kudi na shekarar 2019 ta tsaya har sai an gama gudanar da zaben tarayya da ke gaba ganin yadda Majalisar Dattijai suka dakatar da zaman su har wata mai zuwa.
Majalisar ta kafa baki ga takadar sabon tsarin kankanin albashi da shugaba Buhari ya aika wa Majalisar kamar yadda muka sanar a baya a Naija News da cewa shugaba Muhammadu Buhari yi ce za a mika takardan sabon albashin ma’aikata ga gidan Majalisar.
6. Jam’iyyar ACPN sun bayyana rashin amincewa da janyewar Ezekwesili daga takarar shugaban kasa don marawa Buhari baya
Jam’iyyar Allied Congress of Nigeria (ACPN) sun gabatar da rashin amincewar su game da matakin da ‘yar takaran shugaban kasa Oby Ezekwesili ta dauka na janye wa tseren takarar don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya.
Jam’iyyar sun zargi Ezekwesili da cewa ba ta sanar da su ba kamin daukar irin wannan matakin.
7. Kungiyar Iyamirai ‘Ohanaeze’ sun amince da Atiku PDP a matsayin zabin su ga takara
Kungiyar al’adun gargajiya ta Igbo, ‘Ohanaeze Ndigbo’ ta amince da Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a matsayin nasu zabi ga zaben shugaban kasa da ke gaba.
Kungiyar sun bayyana wannan ne a ranar Alhamis da ta gabata a zaman tattaunawar su na Imeobi.
8. Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga dokar kulawa da mutanen da ke da nakasar jiki
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun sa ga wata sabuwar doka da ke kare mutanen da ke da nakasa.
An sanar da hakan ne ta bakin babban mataimakin shugaban kasa ga lamarin gidan Majalisar Dattijai, Mista Ita Enang.
9. Hukumar INEC ta yi watsi da shirin Adebutu, dan takarar Jam’iyya PDP a Jihar Ogun
Hukumar kadamar da zaben kasa (INEC) ta ce duk wani dan takarar Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun da ke gudanar da yakin neman zabe ba tare da sunan shi na cikin sunayen da hukumar ta gabatar ba, duk aikin banza ce, ba ruwar hukumar da wannan shirin.
Mun sami sani a Naija News da cewa Kwamishinan yada labarai na Hukumar INEC, Mista Festus Okoye ne ya gabatar da wannan a wata gidan radiyo da ke a Jihar Ogun.
10. Mahara da Bindiga sun kame wani Dan Takaran Gidan Majalisa na APC a Jihar Edo, Michael Ohio
Mun sami rahoto a Naija News Hausa da cewa masu Hari da Bindiga sun kame wani dan takaran Gidan Majalisa na Jam’iyyar APC a Jihar Edo, mai suna Michael Ohio-Ezomon.
An sami tabbacin hakan ne daga bakin Ciyaman na yankin, Mista Frank Illaboya wanda ya bayyana ga manema labarai a yankin Eme-Ora a ranar Alhamis 24, ga Watan Janairu, 2019 da cewa Mahara Ukku ne suka sace Michael a misalin karfe 1:00 na Asuba’i a ranar Alhamis da ta gabata.
Ka sami karin labaran Najeriya daga shafin Naija News Hausa