Connect with us

Uncategorized

Yadda ‘yan ta’adda suka hari Sanata Rabiu Kwankwaso a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Farmakin da ya faru a Jihar Kano ya dauke rayukan mutane da dama

‘Yan adawa sun hari tsohon gwamnan Jihar Kano da kuma shugaban jam’iyyar PDP ta Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a yayin da yake gudanar da hidimar neman zaben sa a kuayan Kofa da ke a karamar hukumar Bebeji ta Jihar Kano.

Mun iya ganewa a Naija News Hausa da cewa farmakin ya tashi ne sakamakon tarin hanya da ‘yan adawan Jam’iyyar APC  suka yi wa Rabiu Kwankwaso a lokacin da yake kan yawon neman zabe a Jihar.

Rahoto ta bayar ne da cewa Sanata Kwankwaso da Abba Yusuf, dan takaran gwamnan Jihar sun shirya ne da zagayen rali don neman kuri’u a yankin Kiru da Bebeji a ranar Alhamis da ta gabata amma sai ‘yan adawa suka tare su a hanyar shiga Kofa inda farmakin ya tashi tsakanin jam’iyu biyun.

An bayyana da cewa ‘yan adawan da suka tare Kwankwaso na matsayin magoya bayan Abdulmumin Jibrin ne, watau Mamba gidan Majalisar Wakilai na yankin Kiru da Bebeji.

Kimamin motoci 40 aka kone kurmus da wuta a wajen farmakin.

Haka kuma mutane da dama suka sami raunuka, bayan mutanen da suka rigaya da mutuwa wajen harin.

Kakakin jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, Abdullahi Haruna, ya bada tabbacin farmakin ga manema labarai kuma ya fada da cewa hukumar ta watsar da jami’an tsaro a yankin don magance yaduwar fadan.

Ya kara da cewa, ba a iya gane anihin kimanin mutane da suka mutu ba a wajen harin a lokacin da yake bada wannan bayanin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cikin rahoton Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a da cewa ‘yan adawa sun yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso hari a Jihar Kano.