Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Alhamis, 17 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 17 ga Watan Oktoba, 2019

1. Shugaba Buhari ya takaita tafiye-tafiyen Ministoci zuwa Kasashen Waje

A kokarin shawo kan yaduwar kashe-kashen kudi da kuma kawo inganci ga tafiyar da albarkatun gwamnati, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bada umarnin aiwatarwa da takaita kashe-kashen kudi da ake yi kan ministocin kasar da kuma sauran manyan ma’aikata.

An sanar da wannan ne a cikin wata sanarwar manema labarai a ranar Laraba, wacce Daraktan Bayanai ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Willie Bassey ya sanya wa hannu.

2. Gwamnatin Tarayya Na Shirin Rage Albashin Gwamnoni da Wasu Shugabannai a Kasar

Ministan kwadago da daukar Ma’aikata a kasar Najeriya, Mista Chris Ngige, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na duba albashin ma’aikatan siyasa a kasar hade da ta gwamnoni.

Naija News bisa rahoto da manema labarai suka fitar, Ministan yayi wannan sanarwar ne a Abuja ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin membobin kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomin Najeriya (NULGE) yayin wata ziyarar da suka yi a Ofishin sa.

3. Majalisar Dattawa sun sake Tattauanawa da Diban Kasafin Kasa na 2020 a karo ta biyu

Majalisar Dattawar Najeriya a karo ta biyu sun sake zartawa kan Kasafin kudin shekarar 2020 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a yayin taron majalisar.

Naija News ta tuno da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N10.33trillion za gabar Tarayyar Gidan Majalisan kasar gaba daya domin dubawa da amincewa.

4. Mafi karancin albashi: Kungiyar NLC sun rufe Ofisoshinsu da Makarantu a Delta

A ranar Laraba da ta gabata, kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), reshen jihar Delta, ta rufe ofisoshi da makarantu a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Naija News ta fahimci cewa rufe makarantu da ofisoshin ya biyo ne gabanin zancen yajin aikin da aka shirya kan jinkiri wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi da Gwamnatin Tarayya ke yi.

5. Babban Kasuwa a Onitsha ya kame da Gobarar Wuta

A ranar Laraba da ta wuce, wata mummunar gobarar wuta ya mamaye babbar kasuwar Onitsha bayan da wata motar Man Fetur da ke dauke da (PMS) ta rutsa ga shingen Asibitin Toronto, da ke a Upper-Iweka, Onitsha.

Naija News ta fahimci cewa gobarar ta fara ne bayan da man da motar ke dauke da shi ta warwatse a ko ta ina, daga nan ta haska da wuta.

6. Rikici akan Daukar Ma’aikata a Sirance a cikin Majalisar Dattawan Najeriya

Matakin da kwamitin Majalisar Dattawa ta dauka game da binciken manyan laifukar bada matsayi ko aiki da ya shafi wasu kananan hukumomin gwamnatin tarayya ya haifar da rashin jituwa a majalisar.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa wasu daga cikin hukumomin da abin ya shafa sun karkatar da wasu matsayi ga wasu manyan hafsoshin.

7. Najeriya Za Ta Zama Kamar Kasar Venezuela Idan Aka Cika ga Buƙatar Mafi ƙarancin Albashi – FG

Ministan kwadago da ayuka a Najeriya, Chris Ngige, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai lalace kamar ta kasar Venezuela idan Gwamnatin Tarayya ta biya bukatar kungiyar kwadago akan sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata.

Naija News ta ba da rahoton cewa Ministan kwadago da ayukan kasar, Ngige ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata, ranar da Gwamnatin Tarayya da wakilan kwadago suka sake tattaunawa kan cika aiwatar da sabon mafi karancin albashin.

8. Mamman Daura: Kada kayi Yakin da Ba Zaka Iya Cin Nasarar sa ba – Aisha Buhari ta yi gargadi

Wani babban Magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari da ta guji duk wani nau’in adawa da Mamman Daura.

Magoya bayan wanda aka gane da suna Ibrahim Ali Gombe, ya bayar da wannan korafin ne a wata wasika da ya wallafa a ranar 15 ga Oktoba a shafin Facebook na sa wanda.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa